Za a riƙa ƙara farashin fetur bayan tashin Dala – IPMAN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD 

Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta bayyana cewa, farashin man fetur zai cigaba da hauhawa a Nijeriya bayan da kuɗin Dala ke ƙara tashi.

A wata hira da manema labarai, Shugaban IPMAN na Ƙasa, Chinedu Okoronkwo, ya ce, farashin man fetur ɗin zai cigaba da ƙaruwa muddin Dalar Amurka ta tashi a kasuwar canji.

Ya ce, “ya kamata ’yan Nijeriya su fahimci cewa, idan aka cire tallafin man fetur, gwamnati ba ta ƙayyade farashi ba, sai dai yadda kasuwa ta kama.

Ana sayen kayan man ne a daloli. Dala tana kusa da Naira 890 a Dala ɗaya yanzu. Yayin da Dala ke hauhawa, farashin man fetur zai cigaba da hauhawa, domin da ita ake sayo tataccen a waje.”

A matsayin mafita, ya buƙaci gwamnati da ta ruɓanya ƙoƙarin ganin an samar da iskar gas (CNG) ga ’yan Nijeriya.

“Ya kamata gwamnati ta yi ƙoƙarin ganin ta samar da iskar gas ta CNG ga ‘yan Nijeriya,” inji shi.

Sakamakon haka, ana sa ran farashin man fetur zai wuce Naira 617 a kowace lita da ake sayarwa yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *