Za a Shirya Taron Hadin Guiwa na Kungiyoyin Arewa, A Kan Matsalar Tsaro

Wasu kungiyoyin Arewacin kasar nan, zasu shirya wani taron gangami a garin Kaduna kan matsalar tsaro a Arewa.

Taron wanda za a fara shi a ranar Litinin 15 ga watan Disamba na wannan shekara, zai yi bita ne a kan matsalar tsaro a yankin.

A wata takardar da gamayyar kungiyoyin ta fitar, mai dauke da sa hannun kakakinta malam Abdulazeez Sulaiman ta ce, taron zai samu halartar masana daga fannin tsaro, kungiyoyin al’adu da na gargajiya, kabilu, gwamnati, matasa da mata daga dukkan jihohi 19 dake yankin, domin su tattauna yadda za a hada kai, wurin tunkarar matsalar tsaro bai daya a Arewa. Haka kuma taron zai yi kokarin ganin a samar da kungiyoyin tsaro a kowane sashi na yankin, tun daga matakin kauyuka zuwa jihohi.

Takardar dai ta caccaki gwamnatin tarayya, akan irin rikon sakainar kashin da kuma halin ko in kula da suka nuna, a lokacin da waki’ar Zabarmari ta faru, inda yan Boko Haram suka kashe manoma yan kwadago sama da 100.

Takardar dai ta zargi mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu akan wasu kalamansa da yayi a game da kisan. Ta kuma nuna rashin jin dadin ta ga maganar da babban hafsan rundunar sojin kasa Leftana Janar Tukur Buratai yayi, inda a kwanakin baya aka hakaito cewa, babban hafsa ya ce, zaa shafe shekaru 20, kafin a shawo kan matsalar Boko Haram a Arewa maso gabas.

“Irin kalaman gatsali da suka fito daga bakin Garba Shehu, da Lai Mohammed, da kuma maganganun da Buratai yayi, sun nuna cewa, zancen da gwamnatin Buhari take na karya kashin bayan kungiyar yan ta’addan Boko Haram, ta zo mu ji ta ce kawai. Ya na kuma nuni da cewa, jami’an tsaro sun mayar da yakin ya zama wani shago ne na cinikayya da suke diban kazamar riba”.

Takardar ta kara da cewa ” Matukar gwamnatin tarayya ta kasa daukan kwararan matakai, to aniyar ta ta samar da wadataccen abinci, kan iya shiga wani mawuyacin hali”.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*