Za a soma cin tarar N100,000 kan masu kada bishiyoyi ba da izinin gwamnati ba a Abuja

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Abuja ta ce haramun me ga mazauna birnin su kada bishiyoyin cikin gidajensu da na wuraren da jama’a ke haɗuwa suna shakatawa ba tare da izinin gwamnati ba.

Hukumar ta yi gargaɗin duk wanda ta kama da laifin take wannan doka, tarar N100,000 lakadan ta hau kansa.

Darakta a Hukumar, Hajiya Riskatu Abdulazeez ce ta bayyana hakan a Abuja a ƙarshen mako.

A cewarta, da zarar bishiyoyin da aka daddasa a gidaje suka girma, shi kenan sun zama mallakar gwmamnati wanda dole sai da izinin gwamnatin kafin a sare ko a kada su.

Ta ce ɗaukar wannan mataki ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen kare birnin tarayya daga fuskantar matsalar sauyin yanayi. Don haka ta ce gwamnati ba za ta lamunci sakacin da ka iya jefa rayukan al’umma cikin haɗari ba.

Ta ci gaba da cewa, idan mutum ya samu izinin sare bishiya a wajen gwamnati, to, da sharaɗin za a da wasu guda biyu a madadin wadda aka sare.

A cewarta, bishiyoyi na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma, saboda baya ga taimakawa wajen iskar da ake shaƙa, haka nan suna ƙawata wuri da kuma hana aukuwar sauyin yanayi da sauransu.