Za a soma gwanjon duk shanun da aka kama da lalata gona a Ondo

Daga WAKILINMU

Gwamnatin jihar Ondo ta ce daga yanzu za ta riƙa gwanjon duk shanun da ta kama da laifin ɓarna a gona tare da hukunta masu shanun a bisa umarnin kotu.

Shugaban ‘yan bangan Amotekun na jihar, Cif Adetunji Adeleye, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar sakin shanu sama da 250 da Amotekun suka kama a Akure, babban birnin jihar.

A cewar Adeleye Amotekun ta kama shanu sama da 250 a cikin jihar biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da manoman yankin Ipogun da Ilara da Owena Dam a ƙaramar hukumar Ifedore ta jihar suka yi.

Da yake ƙarin haske kan ɗaukar matakin, Adeleye ya ce duk makiyayin da aka kama da aikata ɓarna a gona za a gurfanar da shi sannan shanun su zama mallakar gwamnati.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a jihar, Alhaji Garba Bello, ya sanya hannu a madadin makiyaya, yayin da Mista Odeyemi Joseph da wasu mutum uku suka sanya hannu a madadin manoma a yarjejeniyar da aka cim ma tsakananin manoma da makiyaya a jihar.

Alhaji Bello ya ba da tabbacin cewa makiyayan za su martaba yarjejeniyar da aka cim ma, yayin da Odeyemi ya yi ra’ayin cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar ɓarna da dabbobi ke yi wa gonaki a jihar.