Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban kwamitin kuɗin da gyaran haraji na Fadar Shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya yi ƙarin haske kan daftarin dokar gyaran haraji wanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa, inda ya ce an tsara daftarin ne ta yadda za a rage wa ma’aikata kaso 90 na harajin da suke biya.
Ya kuma ce daftarin dokar an yi shi ne domin sake daba fasalin harajin ɓAT domin daidaita abin da kowacce jiha ya kamata ta samu ta la’akari da abin da ake samarwa a jihar.
Mista Oyedele ya yi wannan ƙarin haske ne a ranar Laraba a yayin amsa gayyatar majalisar dattawa domin gamsar da ita kan amincewa da wannan daftari.
A watanni biyu da suka wuce, Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya aike wa da majalisun Nijeriya, daftarin dokar gyaran fasalin harajin na 2024.
Daftarin dokokin sun haɗa da: ƙudurin dokar haraji ta ta Nijeriya ta 2024; ƙudurin dokar samar da hukumar haraji ta ƙasa (NRS); ƙudurin dokar kula da haraji da ƙudurin dokar tattara haraji ta haɗin guiwa.
ɗaya daga cikin dokokin ya ƙunshi sauya fasalin ɓAT ta hanyar rage kason gwamnatin Nijeriya daga kaso 10 zuwa 15. Haka kuma irin wannan tsari na kasafi zai shafi sauran jihohi.
Sai dai an ƙalubalanci wannan daftarin doka ta hanyoyi da yawa.
ƙungiyar Gwamnonin Arewa, a yayin taronta a watan da ya gabata, sun bayyana cewa wasu daga cikin abubuwan da harajin ya ƙunsa sun ci karo da muradan yankin, inda suka umarci ‘yan majalisun da suka fito daga jiihohinsu da su yi watsi da shi.
Haka kuma Majalisar Tattalin Arziƙi ta ƙasa (NEC), wadda ta ƙunshi gwamnoni bisa jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, su ma sun buƙaci shugaban ƙasa ya janye wannan ƙuduri daga gaban majalisun Nijeriya. Sai dai Shugaba Tinubu ya kafe kan wannan ƙuduri, inda ya ce a bar majalisa ta raba gardama a kansa.
A yayin da yake yi wa sanatocin Nijeriya bayani, Mista Oyedele, ya ce, waɗannan ƙudurori idan suka amince da su, kaso 30 na ‘yan Nijeriya da ke samun albashi tsakanin N50,000 zuwa N70,000 a wata za cire su daga biyan harajin gwamnati saboda ƙudurin ya ayyana su a matsayin talakawa.
“Za a yanke wa ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu haraji da kaso, 90 wanda hakan ke nufin kusan kaso 30 na ‘yan Nijeriya da ke ƙarɓar mafi ƙarancin albashi na Naira 50,000 da 60,000 da 70,000”.”
“Idan mutum yana samun Naira miliyan 100 duk wata, abin da zai biya na Haraji shi ne kaso 25. idan suna wata ƙasa kamar Afirka ta Kudu, mutum zai biya kaso 41, idan suna kenya, za su biya kaso 35. Idan kuma suna Amurka ko Ingila, za su biya kaso 40 ne, amma mu Njeriya kaso 25 mutum zai biya”.
Game da tsarin rabon harajin ɓAT, mista Oyedele ya ce gyaran dokar haraji ya nuna cewa kowacce jiha za ta samu kasonta ne na iya abin da ka samar a jihar kuma jihohi na da ikon karɓar harajin ne kan siye da siyarwa, amma ba za ta karɓi haraji kan kan kayan da ake shigowa da su ko hidimomi da suka shafi ƙetare ba. Wannan kason ne na gwamnatin tarayya.
“Abu na farko shi ne kowacce jiha za ta karɓi ƙasa da abin da take samu a yanzu. Na biyu, kasuwanci zai gamu da ƙalubale, domin ka sai abu a Kaduna za ka sayar da shi a Abuja,” ya bayyana.
Shugaban kwamitin ya kuma buga misali da ƙasar Amurka inda gwamnonin jihohi ke karɓar haraji kan kayayyakin saye da sayarwa kuma ba su da ikon karɓar wani haraji kan kuɗin shigo da wani kaya daga ƙetare ko wata hidima makamanciyar wannan.
Don haka, da zarar an amince da wannan doka, idan jihohi za su karɓi ɓAT daga ranar, ba su ba kuɗin abin da ya shafi kayan da aka shigo da su daga ƙetare ta jihohinsu. Sai dai abin da ya shafi kasuwanci na saye da sayarwa. “Don haka, gwamnatin tarayya ita ce za ta fi cin moriyar wannan tsari,” in ji shugaban kwamitin.
Ya ce, wannan tsari zai samar da daidaito da kuma hana gwamnatocin jihohi zuwa kotun ƙoli domin neman a ba su damar kafa nau’in harajinsu.
Mista Oyedele ya ce za a sake duba batun tsarin kasafta kuɗi tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi.
Tsarin da ake da shi da shi ne gwamnatin tarayya tana da kaso 15%, jihohi suna da kaso 50% inda ƙananan hukumomi suke da kaso 35.
Ya ce tsarin da za a dawo shi yanzu shi ne gwamnatin tarayya tana da kaso 10, jihohi suna da kaso 55, sai ƙananan hukumomi kaso 35 inda kaso 60 za a raba shi ne tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi bisa la’akari da yadda aka tattara harajin.
Sannan za a yi amfani da ragowar kaso 5 na kuɗin harajin wajen tabbatar da babu wata jiha da ta karɓi ƙasa da bin da aka tsara za ta karɓa a bisa dokar haraji ta 2024.