Za a yi wa Magu ƙarin girma duk da mummunan rahoton da kwamitin Salami ya shirya a kansa

*Fadar Shugaban Ƙasa ta nuna damuwarta kan lamarin

Daga BASHIR ISAH

Bayanan da Manhaja ta samu na nuni da Hukumar Aikin Ɗan Sanda (PSC) na shirin yi wa tsohon shugaban riƙo na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗ’i, Ibrahim Magu, ƙarin girma a bakin aiki zuwa muƙamin Mataimakin Babban Sufeto (AIG).

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta nuna damuwarta kan lamarin, saboda a ganinta tamkar PSC ta bijire wa mummunan rahoton da kwamitin bincike ƙarƙarshin Ayo Salami ya shirya a kan Magu ɗin ne, lamarin da ka iya ɗaukar hankalin ‘yan ƙasa ya kuma haifar da cece-cece-ku-ce, ya zamana an yi wa mai lafi sakayya da kyakkyawa.

Magu wanda aka yi wa ƙarin girma a bakin aiki zuwa muƙamin kwamishinan ‘yan sanda a 2018, kwamitin Jastis Ayo Salami ya ba da shawarar a cire shi daga muƙamin shugaban EFCC tare da neman a hakunta shi bisa zarge-zargen yin amfani da ofishinsa wajen aikata ba daidai ba.

Kwamitin ya buƙaci a tunɓuke Magu daga kujerarsa saboda gazawar da ya yi wajen ba da cikakken bayani game da yadda ya sarrafa kason kuɗi N431,000,000.00 da aka bai wa ofishinsa don gudanar da ayyukansa tsakanin Nuwamban 2015 zuwa Mayun 2020.

Kazalika, an zargi magu da zama silar ɓacewar wasu shaidu ko hujjoji, haifar da tsaiko a shari’a da kuma daƙile kamun da ya kamata a yi wa wasu masu laifi da suka haɗa da wani tsohon shugaban Majalisar Dattawa da sauransu.

Har wa yau, an zarge shi da wahalar da shari’a daban-daban da suka shafi wasu tsofoffin gwamnoni huɗu, wanda ɗaya daga cikinsu sanata mai ci ne a yau.

Daga cikin shawarwarin da kwamitin binciken ya bayar, har da buƙatar a miƙa Magu ga Babban Sufeton ‘Yan Sanda don ɗaukar matakin ladabtarwa a kansa yadda ya kamata.

Sai dai tun bayan da kwamitin ya miƙa rahotonsa zuwa yau kaɗan daga cikin shawarwarin da ya bayar aka aiwatar.

Ana haka ne sai aka naɗa wa EFCC sabon shugaba a Fabrairun 2021, wato Abdulrasheed Bawa, inda bai tsaya wata-wata ba ya buƙaci galibin jami’an ‘yan sanda da aka tura aiki a hukumar su koma babban ofishin ‘yan sanda.

An sauke Magu ne tun daga lokacin da kwamitin ya soma bincikensa, wanda da alama Magu ɗin yana daga cikin ‘yan lelen shugaban hukumar PSC, Musiliu Smith, wanda tsohon Sufeto Janar ne daga jihar Legas.

Tuni dai aka ce wasu manyan jami’an ‘yan sanda suka shiga murza gashin bakinsu tare da ƙorafe-ƙorafe saboda rashin ladabtar da Magu da ba a yi ba. Magu dai ya musanta zarge-zargen da aka yi masa na aikata ba daidai ba.