Daga USMAN KAROFI
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga ‘yan jarida a Najeriya da su riƙa faɗin gaskiya ga masu mulki ba tare da nuna adawa da gwamnati ba. Yayin da yake jawabi a taron ƙaddamar da littafin “Persona Non Grata,” wanda ƙwararren ɗan jarida Ismail Omipidan ya wallafa, a Ladi Kwali Hall, Abuja Continental Hotel, a ranar Asabar, Shettima ya jaddada cewa ‘yan jarida su zama lamirin ƙasa ta hanyar haɗin kai da gaskiya, tare da kaucewa son zuciya.
Ya ce don a gina ƙasa mai kyau, musamman ma ta fuskar siyasa, ana buƙatar ‘yan jarida masu ƙwarin gwiwa waɗanda za su iya yin gaskiya ga masu mulki. Mataimakin shugaban Ƙasan ya kuma bayyana cewa haƙiƙanin ƙarfin zuciya na ‘yan jarida yana cikin gujewa kamewa ko sauyi yayin bin gaskiya, yana mai cewa: “Ana buƙatar jarumai a fagen jarida waɗanda za su zama lamirin shugabanni da sauran masu tasiri wajen ci gaban al’umma.”
Shettiman ya yaba wa marubucin littafin, Ismail Omipidan, bisa juriya da gaskiya da ya nuna a aikin jarida, tare da bayyana littafin nasa a matsayin darasi ga masu jarida da sauran masu tasiri. Taron ya samu halartar jiga-jigai da dama ciki har da Ministan harkokin tekun ruwa, Alhaji Isiaka Oyetola, wanda ya yaba wa marubucin bisa ƙwarewa da rikon amana da ya nuna a rayuwarsa.