Daga DAUDA USMAN a Legas
Shugaban ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Masu Gudanar da Harkokin Kasuwancin Tireda na ƙasa, reshen Jihar Legas, Alhaji Umar Damma ya bayyana cewa shi da sauran mambobin ƙungiyarsa za su cigaba da gudanar da harkokin kasuwancin tireda a cikin tsafta da adalci a Legas da kewayenta gabaɗaya.
Shugaban ƙungiyar, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Yabo da ke cikin Jihar Sakkwato mazaunin cikin garin Legas, ya yi wannan tsokacin ne a Legas jim kaɗan bayan kammala taron gudanar da addu’ar ɗaurin auren ‘yar gidan Alhaji Muhammadu ɗan Damma Yabo, Shugaban Kasuwar Doya da ke Kasuwar mile12.
Taron wanda ya samu halartar sarakuna Hausawa na unguwarni daban-daban na cikin garin Legas da manyan malamai da ‘yan kasuwa da sauran al’ummar Jihar Legas bakiɗaya.
Haza zalika, taron ya gudana ne a harabar masallacin Juma’a na kasuwar ‘yan doya mile12 a ranar Lahadin makon jiya.
Bayan kammala taron gudanar da addu’ar ɗaurin auren ne Wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ya keɓe shugaban ƙungiyar masu gudanar da harkokin kasuwancin tireda na Jihar Lega, Alhaji Umar Damma domin domin ji ta bakinsa dangane da harkokin kasuwancin tireda a Legas, inda Alhaji Damma bayan ya kammala taya Alhaji Muhammadu ɗan Damma Yabo murnar samun damar ɗaurar da ɗiyarsa, ya ce, harkokin kasuwancin tireda a halin yanzu sai an haɗa shi da haƙuri idan aka yi la’akari da yadda rayuwar al’umma ta shiga wani ƙangi na matsatsi, babu daɗi.
Ya ƙara da cewa, “amma duk da hakan za a iya cewa Alhamdulillahi, tun da ana samun cigaban al’amuran kaɗan-kaɗan.”
Ya ce, kuma shida sauran mambobin ƙungiyar tasu ta ‘yan tireda a Legas za su yi iyakar ƙoƙarinsu a wajen cigaba da gudanar da harkokin lasuwancin nasu a cikin adalci, domin kyautata wa rayuwar al’umma.
Ya cigaba da jawo hankulan mambobin ƙungiyar tasa da sauran ‘yan kasuwa da su ƙara ƙoƙari a wajan gudanar da kasuwancin su na yau da kullum a cikin adalci domin samun kyakkyawar riba a nan duniya dama lahira bakiɗaya.