Daga BELLO A BABAJI
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kare batun aikin rusau da ya ke yi a birnin na wasu gine-gine da suka saɓa ƙa’ida.
Ya ce baki ɗaya gine-ginen da suke rushewa an yi su ne a filayen gwamnati ta bi ta haramtattun hanyoyi.
Ya kuma tabbatar da cewa kasancewar ana cecekuce game lamarin, ba sa jin tsoron duk wani sharri da ake yi musu.
Wike ya bayyana hakan ne a yayin taron raba babura ga hukumomin tsaro a sakatariyar hukumar kula da birnin (FCTA), a ranar Alhamis.
Ministan ya ƙara da cewa, babu yadda za a yi mutum ya tsinci kansa a matsayin da yake, kuma ya yi tsammanin ba za a masa sharri ba.
“Akwai masu ƙwacen fili da yawa. Wasunmu sun zo ne su shimfida ƙafafunsu. Sama ta rikito. Zai ma fi ace sama ta rikito ta yadda ba za mu riƙa gaggawar zuwa ba”, inji Wike.
A ƴan watannin nan ne FCTA ta ƙudiri aniyar rushe duk wasu haramtattun gine-gine da aka yi a birnin da kuma waɗanda aka yi su ba bisa ƙa’ida ba.
Duk da cewa lamarin ya tada ƙayar baya da ta kai ga wasu sun fara zanga-zanga, amma ministan ya tirje tare da cewa babu ja da baya game da hakan.