Daga RABI’U SANUSI
Wakilin Ƙananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar Wakilai, RT Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya bayyana cewa zai cigaba da samo guraben aiki ga matasan yankunan ƙananan hukumominsa a matakin Tarayya musamman a ɓangarorin aikin tsaro.
Rurum Wanda shine Shugaban Kwamitin Kula da harkokin Sojin sama na Majalisar ya bayyana hakan a wajen taron yaye sabbin dakarun Sojin sama da suka kammala karɓar horo a garin Kaduna.
Ɗan majalisar ya ce cigaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa da tallafa musu samun aikin zai ƙara inganta sha’anin tsaro dake fuskantar ƙalubale a kasarnan.
Ya ce a wannan karon matasan yankin ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure aƙalla 16 na cikin waɗanda aka yaye kuma sun zama cikakkun dakarun Sojin Najeriya.
A cewarsa, shekaru shida da suka gabata duk shekara baya gaza samar wa yara 15 zuwa 20 aikin na ‘Yan Sanda, Civil Defence da ɓangarorin soji waɗands kuma ciki har da mace ta farko a tarihin Kano ta Kudu da ta shiga aikin sojin sama a bara, wato Hindatu Isa Rano.
Ya buƙaci matasan da su sanya tsoron Allah a zukatansu tare da kasancewa jakadu na gari a duk inda aka tura su aiki.