Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Manajan Darakta na hukumar yawon buɗe idanu na Jihar Kano Hon. Tukur Bala Sagagi ya bayyana cewa damar da ya samu na kula da hukumar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba shi ya ji daɗi, dama ce da zai taimaka wa al’umma, yarda da ƙauna ce tasa aka kira shi aka ce ya zo ya yi.
Ya ce abin dai kuma abin rashin daɗi shi ne yadda suka taras da abubuwa sun lalace sun ragargaje ba ɗa’a, ba ƙima ba tsafta, ba kayan aiki a hukumar.
Ya ce abin mamaki kwamfuta wannan ta buga takarda babu ko guda ɗaya, duk takardar da za a buga ba sirri sai dai aje waje a yi duk fayil dake hukumar akwai ta a waje.
Ya ce wannan abin takaici ne da tozarta kai, “an cuci al’ummar Kano, an zalunce su da hakan ya faru ne saboda rashin shugabanci nagari, da akwai shugabanci nagari da duk wannan shaƙiyanci ba za a yi ba.
“Amma tunda daga sama a lalace take ba abinda ta sani illa a kawo mata, abinda suka sa a gaba kenan a yi aiki ko kar a yi ba abinda ya dame su a gwamnatin baya.”
Ya ce zuwansa akwai ƙungiyar masu otel na Kano sun kawo masa ziyara sun koka da rashin damuwa da halin da suke ciki illa a zo a karva a wajensu a riqa tozartasu da muzantasu.
Manajan daraktan na hukumar yawon buɗe idon Tukur Sagagi ya ce Kano ta yi fice a duniya akan al’ada, za su yi ƙoƙari su bunƙasa yawon buɗe ido na al’adu, ba wata ƙasa ta duniya da za ta ja da Kano akan kyawawan al’adu, su za su tallata su jawo mutane su zo su gani a haɗu a bunƙasa harkar.
Hon. Tukur Sagagi ya ce akwai tsari da za su bunƙasa na yawon shaƙatawa, kamar kasuwar Kurmi sun yi kira ga Gwamna ya kawo mata ɗauki a ingantata domin duk duniya ba inda za ka samu kaya na al’adar Bahaushe irin na kasuwar kurmi, inji shi.
Ya ce akwai hanya da za a farfaɗo da ita ta fatauci da ake daga ƙasar nan zuwa na Larabawa, za a yi ƙoƙarin a inganta ta, sannan wurare da ake sana’o’i na gargajiya za a samar da wani waje a kawwame duk mai sana’ar gargajiya ya samu waje a wurin ya zama tamkar dandali na kowace sana’a da zai ja hankalin masu yawon buɗe ido.
Sagagi ya ce da taimakon mai girma halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin zai ba su dukkan taimako, Kano sai ta zarce kowace jiha a ƙasar nan a harkar yawon buɗe ido da yardar Allah sai dai ma ta yi gogayya da sauran ƙasashe na duniya.
Hon.Tukur Bala Sagagi ya ce za za su yi amfani da doka ba tare da muzantawa kowa ko ci wa kowa mutunci ba, wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda Gwamna Injiniya Abba Kabir ya ke faɗa shi ma cewa a doron shari’a zai yi aiki da yardar Allah.
Akwai shiri da suke da shi na tattara masu ruwa da tsaki akan harkar yawon buɗe ido a tattauna matsaloli da shawarwari ta yadda za a samu daidaito da kuma samar da haɗin kai don samun ci gaba.