Za mu haɗa kai da al’umma don magance matsalolin da sauyin yanayi ke jawowa – Ɗahiru Muhammad

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Dakta Ɗahiru Muhammad Hashim, Ko’odinetan Ayyuka na Jihar Kano (ACReSAL), ya bayyana cewa za su yi aiki da ya haɗa da wayar da kan al’umma, don magance matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa.

Ya ce, aikinsu na haɗin gwiwa ne a tsakanin Majalisar Dankin Duniya da Gwamnatin Tarayya da jihohi 19 na Arewa da Birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida ciki har da wakilin Blueprint Manhaja, inda ya yi nuni da cewa babban aikin da ma’aikatar take shine na daƙile matsaloli da suka shafi zaizayar ƙasa da hana kwararowar hamada da samar da hanyoyi ingantattu da za su taimaki jama’a akan illoli na canjin yanayi da bada gudummuwar gaggawa akan abubuwan da suka shafi canjin yanayi.

Ya ce zuwansa ma’aikatar ya tarar da ƙalubale da dama, suna aiki akan abubuwa da suka shafi ruwan sha, harkokin noma da muhalli suna da kuma da haɗin gwiwa da ma’aikatun ruwa, gona da muhalli wajen tafiyar da ayyukansu.

Ya ce sun zo sun tarar da jihar Kano an bar ta a baya jihohi da yawa sun wuce gabanta, saboda irin gudummuwar da gwamnatocinsu ke bayarwa.

Wannan na daga abin da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya fahimta shi ya sa ya ɗauke ma’aikatar ya mayar da ita ƙarƙashin ofishinsa don a samu cigaban da ya kamata.

Dakta Ɗahiru Muhammad Hashim ya ce daga zuwansa ma’aikatar sun aiwatar da ayyuka da dama da suka haɗa da kwashe kwatami na sharar kwatoci don kiyaye ambaliyar ruwa ana yin  aikin a ƙananan hukumomi takwas na ƙwaryar birni.

Sannan suna da shiri na raba kayan aiki da suka ƙunshi baro da cebur da takalmin ruwa da safa da takunkumin rufe fuska sama da 2000 ga ƙungoyoyin aikin gayya don cigaba da gudanar da ayyuka.

Ya ce sun samu ma’aikata a cikin koma baya wasu sun shafe wata shida ba albashi amma yanzu an soma biyan su, sannan ba kayan aiki na zamani dan haka suka samarda kwamfutoci da manyan wayoyin hannu IPad da za’a riƙa fita da su filin aiki da kuma samar da intanet mai inganci a ma’aikatar  suna kuma ayyuka dan sanya  injuna masu amfani da hasken rana wato sola da za a ƙaddamar nan kusa.

Dakta Ɗahiru Hashim ya ce sun kuma samar da ɗakin bincike a Jami’ar Maitama Yusuf wanda  ɗaliban kimiyya za su yi amfani da shi don inganta karatunsu.

Ya ce suna da shirin yin  ayyuka na samar da dama-damai da gyara wasu sun ziyarci dam na Tiga sun ga matsaloli da za’a gyara sun sami dam da ma’aikatar ta yi a Yansabo sun ga matsaloli dake damunsa da yanda za a gyara domin al’umma su cigaba da amfana.

Ya ce su ma ma’aikata suna buƙatar kyautatawa da biya musu haqqinsu su kuma sai su yi ayyuka da ya kamata a ce sun yi kuma zuwansa ya na ƙoƙarin ganin an kyautata musu kuma suna yin aiki tuƙuru.

Dakta Ɗahiru Hashim  ya ce babban fatansa a ma’aikatar shine a cikin shekara ɗayansa  na shugabantar ma’aikatar wanda  aiki ne na tsawon wa’adin shekaru shida a lokacin da za su cika shekara ɗaya a ofis jihar Kano ta zama kan gaba wajen amfanar shirin don bunƙasar cigaban al’ummar Kano.