Za mu haɗa kai da kamfanoni don samar wa ’yan kasuwa gurbi a Kano, cewar Sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Saida Waya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Injiniya Abubakar Usman Ahmad, sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar masu sana’ar sayar da wayoyi a kasuwar titin Berut, ya bayyana cewa za su yi ƙoƙari wajen kawo sauye-sauye masu nagarta don bunƙasa ci gaban masu sana’ar sayar da wayoyi a kasuwar.

Ya ce Allah ne ya ƙudurta shi zai samu nasara a zaɓen da aka yi, ba domin ya fi kowa ba, sai dai haka Allah ya so, don haka abokan kawo canji da suka yi takara tare su zo su ba shi haɗin kai da goyon baya, don haɗa hannu domin kawo ci gaba a kasuwar, inji shi.

Injiniya Abubakar ya ce suna da dillalai na kamfanin waya kusan 10 a kasuwar titin Bairut, amma wani lokacin kaya kan yanke musu, don haka za su yi ƙoƙarin haɗa kai da kamfanoni domin ‘yan Kano su samu gurbi wajen kowane kamfani don bunƙasa kasuwancin waya.

Ya ce yanzu babbar matsalar da take damunsu a harabar kasuwar shi ne wajen ajiye abubuwan hawa, musamman ga abokan cinikinsu da ke shigowa, da kuma harkar tsaro suna daga manyan matsalolin da ke tayar musu da hankali. Kuma cikin yardar Allah za su yi shiri don shawo kan matsalalolin da ke damun kasuwar.

Injiniya Abubakar ya gode wa Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa da Kwamishinan ma’aikatar kasuwanci bisa goyon baya da suke bayarwa don bunƙasa ci gaban kasuwanci a Jihar Kano.

Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar masu sayar da waya da dangoginta na ƙasa wato Mobile Phones and Allied Products Traders of Nigeria, Musa Haruna Mamza wanda su ne suka kafa ƙungiyar ‘yan kasuwar titin Bairut, kuma ɗaya daga iyayen ƙungiyar, a yanzu ya nuna gamsuwa da farin ciki bisa yadda zaɓen ya gudana, tare da jan hankalin ‘yan ƙungiyar su haɗa kai don samun nasarar ci gaban kasuwar.

Musa Mamza ya ce ba wani zaɓe da za a yi a ce ba a samu ƙorafi ba, wani zai ce ba a yi masa daidai ba. Don haka a manta da komai, kowa ya zo a haɗu a sa ci gaban ƙungiyar a gaba don cimma nasarar ta.