Za mu hukunta ƙasashen da suka bijire wa yaƙi da ɗumamar yanayi – MƊD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ɗaukar wani mataki da zai fara hukunta ƙasashen da ke fitar da hayaƙi da sinadaran da ke gurɓata muhalli ba kuma tare da ɗaukar matakin da ya dace ba.

A wata ƙuri’ar jin ra’ayi tsakanin ƙasashe mambobin majalisar mai cike da tarihi da aka kaɗa a ranart Laraba, da tsibirin Vanuatu ya bada shawara, ta kuma tanadi damar gurfanar da ƙasar da aka samu da saɓa wannan doka, gaban kotun duniya musamman idan wannan ƙasa ta yi kunnen ƙashi wajen bada gudunmawa a yaƙi da gurvatar muhalli.

Da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri’ar, Firaministan Tsibirin na Vanatau Ishmael Kalsakau, ya ce, wannan wani al’amari ne mai matuƙar muhimmanci da kuma tarihi, idan aka yi duba da yadda ƙasashe ke faɗin batun yaƙi da ɗumamar yanayi, amma basa hoɓɓasa wajen dakatar da shi.

Kafin fara ɗaukar matakin gurfanar da ƙasashe masu kunnen ƙashi a gaban kotun duniyar, za a fara fitar da tsare-tsaren hukunce-hukunce da za a yanke matuƙar aka samu ƙasa da aikata wannan laifi.

Ko da jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya ke mayar da martani kan zargin dalilin da zai hana bai wa ƙananan kotuna damar yin wannan hukunci, sai ya ce wannan matsala ce da in har ba a ɗauki matakin da ya dace cikin gaggawa ba, tabbas bala’o’in da ke da nasaba da sauyin yanayi za su mamaye duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *