Za mu kashe wutar rikicin da ta turniƙe APC kafin 2023 – Adamu

Sanata Abdullahi Adamu ya kasance shi ne Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, kuma ya riƙe muƙamin gwamnan Jihar Nassarawa har na tsahon zango biyu, kuma sannan tsohon sanata ne da ya bar gado, ya amshi shugabancin jam’iyyar. Ya amshi ragamar jam’iyyar ne daga hannun Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe a watan Maris, 2022, a yayin da wutar rikici ta ke tsaka da ruruwa a cikin jam’iyyar.  A wannan cikin tattaunawar ta musamman da jaridar Daily Trust, Sanata Adamu ya bayyana kyakkyawan fatansa na ganin wutar rikicin da ta ruru a wasu jihohi a jam’iyyar za a kashe su kafin nan da babban zaɓe a shekarar 2023. Sannan ya yi magana a kan mizanin da ya ɗora salon mulkin shugaba Buhari, dalilinsa na goyon bayan shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a yayin zaɓen fidda gwani na takarar shugaban qasa a jam’iyyarsu, da kuma dalilin da ya sa yake da yaƙinin cewa za su ci zaɓe, da dai sauran batutuwa. A sha karatu lafiya. 

A matsayinka na shugaban jam’iyyar APC mai mulki, amma ya aka yi ɗan takararka ya kasa samun nasarar zaɓen fidda gwani? Me za ka ce game da wannan lamari?  
Ban fahimci me kake nufi da ɗan takarata ba. 

Bayanai sun bayyana cewa, ka yi wa ‘yan majalisar Dattawa nune da cewa, shugaban Majalisar shi ne gwaninka, da alama kuma sun yi maka bore. Ya ka ji da hakan ta faru?
Bai kamata ku kalli abin a bai-bai ba. Bayan neman shawarar yan jam’iyya, an samu yaƙinin cewa shi ne gwanin da ya dace. Musamman duba da yadda jam’iyyar PDP ta zaɓo Atiku Abubakar  matsayin ɗan takararta duk da cewa kuwa ya kamata ɗan takarar ya kasance daga kudancin ƙasar kamar yadda suke ta faɗa. Dole mu zaɓo wanda zai kara da shi.

A baya fa ka taɓa kasancewa mamban jam’iyyar PDP,  kuma gwamna a ƙarƙashin tutar jam’iyyar.
Ni ba mamba kawai ba ne, tsohon gwamna ne a ƙarƙashin tutar jam’iyyar. Sannan kuma ni ne sakataren kwamitin amintattu. Amma ga mamakin mutane, lokaci da suka tashi zaɓen fidda gwani na takara, sai suka zaɓi ɗan Arewa, Atiku Abubakar. Wannan ya girgiza mutane. Mutanen da suka ci alwashin cewa, za su fidda ɗan takara daga kudu sun aikata saɓanin hankali, mu kuma me za mu cewa masu zaɓenmu?

Amma ba ka tunanin masu zaɓenku ba a Arewa kawai suke ba, akwai su ma a Kudu. Ko ba haka ba?
Amma mafi rinjaye na ƙuri’un daga can (Arewa) suke. Don haka a take a nan muka sake tunani. Bayan shawarwari muka ga kawai hakan ita ce mafita. Don haka na bayyana musu a matsayinsa na shugaban jam’iyya. Ni ban yi magana da ‘yan majalisa ba. Na tattauna dai da majalisar tafiyar da jam’iyya (NWC) da wasu gwamnoni kuma. Inda suka fi karkata  a kan a kai takarar kudu. Abinda na sani ne, idan kowa a jami’yyar ya ce zai ja tunga, to ba abinda hakan zai kawo sai rikici. Don haka, na ce a shiga zaven fidda gwani kawai. Sun nemi ma na janye kalamaina, amma na ƙi.

A lokacin da shugaban ƙasa ya ce duk mai shawara takara ya tsaya, shi ba shi da gwani, sai muka shiga zaɓen fidda gwani. Yanzu ga shi abin ya zama tarihi. Ɗan takararmu Asiwaju Bola Tinubu shi ya lashe zaɓen. Bayan gudanar da tsaftataccen zaɓe. A take a nan ni da shugaban ƙasa muka damƙa masa tutar jam’iyyar. Sannan kashegari na kwashi magoya bayana muka je har gida muka taya shi murna tare da yi masa mubaya’a. Wannan ita ce matsayata har yau. Kuma da yardar Allah za mu yi nasara.
 
Kana so ka ce kenan matsayarka ta baya a jam’iyyar sam ba ta shafi alaƙarka da ɗan takarar shugaban ƙasar naku ba?
Sam! Amma zan yi magana a kan kaina ne kawai. Na jagoranci wakilai zuwa gidansa dake Abuja kuma mun yi masa mubaya’a. Kuma muna so jam’iyyarmu ta samu nasara. Kuma nasara ba ta taɓa samuwa da rarrabuwar kai. 

Ka na jin kamar an ci amanarka?
A wannan matakin ba ta zancen cin amana ake yi ba. A wannan mataki mai nisa na Jam’iyyar abinda ake magana shi ne, dattaku. Kuma ko me za mu yi muna neman shawara. Amma gwamnoni sun yi abinda ya taɓa min muƙamina, amma duk wannan ya wuce. 

Ka na ganin gwamnonin sun dauki matsayar da suka ɗauka ne saboda son ransu?
Ni fa an kawo ni ne don na kashe gobara. Don haka, bana son tone-tonen baya. Kowa ya gyara ko ya ɓata ya sani. Ina iya ƙoƙarina a matsayin shugaban jam’iyya, amma kuma jam’iyyar ce mai ya ke wuƙa da nama. Na kasance mai sadaukar da biyayya ga jam’iyya. Bola Tinubu shi ne ɗan takararmu. Har ma ya zaɓi mataimakinsa. Kuma dukkanninmu muna goyon bayan hakan. 

Kafin ka zama shugaban jamiyyar, an ɗora maka nauyin sasanta tsakanin mambobin da suka samu saɓani. Yanzu bayan zaven fidda gwani ba buƙatar sasanci. Me za ka ce game da haka? 
Na yarda da kai a wannan batu. Shi sasanci aiki ne da ba ya ƙarewa. In dai kana harka da mutane, dole akwai savani. Mafi yawa saboda jiji da kai, ba daɗi, ba ƙari. Wani kuma ana samu a yayin da wani zai ji shi ba a tsaya an saurare shi yadda ya kamata ba. Ko kuma irin siyasarmu: musulmi da kirista, ƙabilanci, da banbancin addini da makamantansu. Su ma waɗannan matsaloli ne masu zaman kansu.

Ka cigaba da sulhun? 
Kamar yadda na gaya maka, sulhu aiki ne da ba ya ƙarewa. Don haka, kullum muna yinsa. Kuma muna iya ƙoƙarinmu. 

A kwanan nan ne ɗa a wajen Shugaban amsa wanda yake jagorantar kwansitiwensin Shugaban a majalisar wakilai ya tsallake ya bar jam’iyyar APC.  Wannan ɗaya ne daga misalin yawan ficewar da ake yi daga jam’iyyar da mutanen da suke jin an ɓata musu saboda azaɓen fidda gwani. Wanne tsokaci za ka yi game da wannan?
Komai yana da lokacinsa. Hatta lokacin zuwanka Duniya da lokacin barinka. Hakazalika, akwai lokacin dukkan abubuwan nan da muke gani. Ina dai aka yi zaɓen cikin gida na jam’iyya sai ka ga wasu mutane ba su ji dadi ba, wataƙila ko don ba su samu abinda suke so ba. Wannan halin ɗan Adam ne. Shi ya sa sulhu ya zama abu wanda ba ya ƙarewa. Sau da yawa mukan yi imani da Allah a matsayinmu na musulmi ko Kirista, amma wasu lokutan sai mu ƙi yadda da abinda ya zaɓa mana. Don haka, nake jan hankalin shugabancin jam’iyya da kada su gajiya da yin sasanci. Amma sai dai kamar yadda na faɗa, muna sulhunta abinda zai sulhunta kawai. 

Ba ka tunanin yadda ɗa ga shugaban ƙasa ya fice ya bar jam’iyya mai mulki, tamkar kun ɗauki wani babban makaminku na siyasa kun miƙa shi a hannun abokan adawarku a siyasa ne?
Wani lokacin ku ‘yan jarida kun ɗaukar abubuwa ku kai su inda ma Allah bai kai su ba. Kafin na zama shugaban jam’iyyar nan, na ga abubuwa kala-kala a gwagwarmayar siyasa ta. Har ‘yanuwa ciki ɗaya na gani sun raba jam’iyya, wannan ba sabon abu ba ne. Idan wannan mutumin ya ga abinda ya fi dacewa da shi; idan dama ba ta yi masa ba ya koma hagu, ba za a yi masa ƙarfi da yaji ba. 

Ya batun kuma jiga-jigan kamar yan majalisa wato abokan aikinka na da a majalisar Dattawa waɗanda suke ganin an musu ba dai-dai ba?
Idan za ka iya tunawa, bayan zaɓen cikin gida na jam’iyya, ana ta surutu a kan ficewar mutane daga jam’iyyar. Ni da kaina na nemi majalisar don mu tattauna mas’alar jam’iyyar. Amma saboda kasancewar ni ne shugaban jam’iyyar, sai na ɗauki laifin a kaina kuma na ba su haƙuri. Wannan ajizancin ɗan’adam ne.

Ɗan’adam tara yake bai kai goma ba. Dole sai mun koyi yin haƙuri da juna. Wasu daga matsalolin da suka taso har wasu suka faɗi zaɓe sakamakonta, ba ni da hannu a ciki. Amma tunda ni shugaba ne, sai na ɗauki laifin kawai.

Don haka, aka cigaba da sulhu.  Waɗanda suka yi haquri suka jira, za su samu wani abu; ba za su tashi a tutar babu ba. Muna da gwamnati, don haka suna da damammaki da za su iya zuwan musu. Ina da yaƙinin cewa, gara su yi haƙuri su bi abin a sannu maimakon bauɗewa. Ni a wajena wannan ba sabon abu ba ne. 
  
Ka na ganin daga kammala zaɓen cikin gidan duk wani tarnaƙi ya ƙare?
Kamar yadda na ce, akwai wasu damammakin. Wasu ‘yan takarar suna janyewar saboda sulhun da ake yi a matakin jiha da na ƙasa bakiɗaya. 
 
Wanene ɗan takarar jihar Yobe inda shugaban Majalisar Dattawa yake son tsaya wa takara?
Maganar tana kotu, don haka, ba na son cewa komai a kai. Amma mu a wajenmu ba mu sa sunan kowa ba sai shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan. Amma tunda magana tana kotu, ba zan shiga ciki ba. 

Wasu mutanen suna ganin cewa, takarar jam’iyya LP ƙarƙashin jagorancin sojin Gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da kuma sabuwar jam’iyyar Rabiu Kwankwaso ta NNPP, da wuya APC ko PDP su iya kai labari. Kana ganin haka kuwa?
A gaskiya ba na tunanin haka. APC tana ta yaƙi don ganin ta lashe zaɓen 2023. Kuma za mu lashe da yardar Allah. Idan kuma an samu rashin nasara za mu amsa. Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ita ce take da iko a kan wannan. Kuma suna da dokoki da suke amfani da su. Duk abinda ya faru, za mu duba abinda doka ta tanada a kansa mu yi aiki da shi. Amma idan haka Allah ya ƙaddara wa ƙasar nan a 2023, shikenan. 

Ka na nufin wannan ba ya cikin lissafinka a halin yanzu?
Ƙwarai kuwa. A yanzu muna fafutukar samun nasara ne. 

Kamar ba ka da yaƙini?
Na san muna fafutukar cin nasara kuma Allah zai ba mu nasara. Kawai dai abinda muke buƙata mu sa a ranmu za mu iya. Muna jure sauraro irin wannan tsokaci ne kawai don muna cikin dimokuraɗiyya, saboda akwai ‘yanci ko ma me kuke kiransa.

Mun bada ‘yanci ga mutane su yi ra’ayinsu kuma su bayyana shi yadda za su iya. Kuma muna girmama ra’ayoyin in dai an yi su ne a siyasa. Amma ni ina kiran waɗannan kalaman a matsayin, ‘hayaniyar siyasa’, kuma ku ‘yan jarida ku kuka fi ƙwarewa a wannan. Yanzun nan sai ku mai da targaɗe ya zama karaya. Na yarda da batun cewa NNPP jam’iyya ce sananniya Kuma mai rajista. Kuma ko ina so, ko bana so za su tsaya takara.

Kuma eh, za su iya rage mana yawan ƙuri’u, saboda wasu daga cikin mambobinta sun kasance tsaffin hannun ne a siyasa. Kuma saboda rigingimu da aka samu a Kano, shirme ne ma a ce wai ba za a samu varaka da hatsaniya ba. 

Haka zalika, jam’iyyar LP ma za ta rage wa PDP quri’u. Ɗan takarar jam’iyyar an ka da shi a PDP. Sai ya ɗauki takarar ya kai ta wata jam’iyyar don ya farfaɗo da ita, idan kun ba ni dama na yi amfani da wannan zaurancen. Jam’iyyar LP tana da tasiri ne a Kudu maso gabas da kuma wataƙila kudu maso Kudu.

Ba za ka iya cewa hakan wani tasiri ne a siyasa ba. Amma kuma hakan bai isa ya girgiza jam’iyyarmu ko kaɗan ba. APC tana da mambobi miliyan 42 da suka yi rajista da ita a Nijeriya. Kuma a hakan ma ba dukkan ‘yan jam’iyyar ne suka yi rajista ba. Sai dai kuma idan na ce maka sam ba mu da matsala, Ni kaina ns san yaudarar kaina nake yi.
 
Amma kamar ba kwa sulhunta wasu daga cikin manyan matsalolinku. Misali, a Kano akwai yan takarar Gwamna guda 2 daga tsagin daban-daban a jam’iyyar APC?
Ai abinda ya faru a Kano ba a nan kawai ya faru ba. Yana faruwa a wasu jihohi ma.

Kamar tarihi ne yake son maimaita kansa irin na tsohuwar jam’iyyar Buhari ta CPC. Da aka rasa takamaimai ɗan takara. Wannan ya jawo jam’iyyar ta faɗi zaɓe. 
Na yi maka alƙawarin cewa da yardar Allah wanda ya ba mu ikon jagorancin jam’iyyar a yau, za mu sulhunta matsalar kafin nan da kakar zaven mai zuwa. Muna da watanni shidda daga nan zuwa watan Fabrairu. Da yardar Allah za mu tsayar da ɗan takara guda

Yadda ka ke magana wasu mutanen sai su ɗauka kamar ba ka san halin da ‘yan Nijeriya suke ciki ba. Akwai rashin gamsuwa sosai game da yadda abubuwa suke faruwa a ƙasar nan musamman a ɓangarorin rashin tsaro, rashin arziki, da tsadar rayuwa. Ba ka ganin wannan kaɗai ya isa jama’a su yi wa jam’iyya mai mulki tawaye?
Na so a ce zan iya ba bayani a kan ainihin su waye PDP, NNPP da kuma LP. A gaskiyar magana, akwai rashin gamsuwa amma wannan maganar da ka yi ita ta jawo ta. Babu wata jam’iyya ko gwamnatin da za ka ce ba ta da matsaloli. Kuma da ma gwamnati kullum tana amsar albarkacin bakin mutane da suke tofawa. Wasu lokutan za ka ga jam’iyyar adawar ita ce kasasshiyar amma mutane sun fi ganin baƙin jam’iyyar gwamnati mai mulki. Don haka, mu ma muna da namu matsalolin kamar sauran gwamnatocin.

’Yan Nijeriya sun ce ba su tava jin jiki kamar wannan lokaci ba. Me za ka ce?
A gaskiyar magana, ku ‘yan jarida kun fi ganin kuskure a inda yake akwai alkhairi a cikin abubuwan da gwamnatin ta yi. Akwai matsala sosai a kan yada kuke abubuwa. Misali, jam’iyyar PDP ta shafe shekaru 16 a kan mulki amma yaran makaranta suna fama da matsalar rashin abinci. Amma wannan gwamnatin ta samar da shirin ciyar da ‘yan makaranta. Kuma ana ta gudanar da shirin tsahon shekaru. Amma wannan ba damuwarku ba ne. 

Ya kuma iyayen da ba sa iya samun abinci saboda talauci fa?
Tsaya ka ji. Ayyukan ray ƙasar da ake yi a ƙasar nan a yanzu rabon da a yi su tun shekaru 20 baya. Sai bayan zuwan Buhari ne aka samu. Kalli yawan titunan da gadojin saman da aka gina, wasu kuma aka gyara. Ya batun tasar jirgin ƙasan Nijeriya wacce ta kusa macewa murus? Yaran da suke ƙasa da kai a makarantar sakandare ba za su taɓa sanin ma meye digar jirgin ƙasa ba sai dai idan sun ganshi a littafi. Amma yanzu sufurin jirgin ƙasa ya dawo kai’n da na’in a ƙasar nan. 

Me ya sa kullum ba kwa ganin alkhairan gwamnati? Kun fi so kullum ku samu abinda za ku yi suka don ku taimaka wa ‘yan adawa su yi kamfe da shi?
Mun samu rahotanni a kan yadda aka kulle tashar jirgin ƙasa saboda rashin tsaro. Sannan game da shirin ciyar da ‘yan makaranta, wasu yaran suna samun abinda za su ci, amma da yawa daga iyayensu ba sa samun abinda za su ci saboda yanayin da ƙasar take ciki. Ba ka ganin ba jaki aka bari ake dukan taiki ba?

Me za ka ce game da shirin cigaban al’umma da wannan gwamnatin ta kawo. Shiri ne mai kyau, sai dai kuma mutane ƙalilan ya shafa. Kuma su kaɗai suke amfana da shirin?
Da ma ai kowa yana abu dai-dai yadda zai iya. Nan kuma kana maganar abubuwan da gwamnati ta yi da wanda ba ta yi ba. Amma ka tava la’akari da inda gwamnatin za ta samo kuɗaɗen da za ta aiwatar da abubuwan da kake faɗa? Ba wanda yake wannan zance.

Akwai shirgegen bashi a kan Nijeriya. A halin da ake ciki ma ministar kuɗin ta ce idan da za haɗa dukkan kuɗaɗen shigar ƙasar sai ma ka ƙara da ranto wasu kuxaxen don biyan bashi. Waɗannan su ne matsalolin. Me kake gani to?
Zan iya tunawa na taɓa cewa, ba ni da ƙorafin a kan surutu da ake yi a kan rancen da gwamnati take yi. Gwamnati za ta iya cigaba da rance har gaba da abada.

Ba Nijeriya kaɗai ke aro ba. Sauran ƙasashen Duniya ma suna yin rance daga bankin Duniya da sauran wurare. Abinda zan damu shi ne, idan ba a yi amfani da kuɗin yadda ya dace ba. Duk ayyukan cigaba da muka samar a garin nan daga nan muka samo kuɗaɗen. Sannan ya kamata a gode wa gwamnati yadda ta samar da kuɗaɗen shiga.

Man fetur da shi  ne kaɗai  hanyar samar da kuɗin shiga, yanzu muna son hanyoyin da za mu canza. Matsalolin da suke kawo rashi samuwar kuɗin shigar, ba daga gare mu ba ne. Duk yadda muke ƙoƙartawa, sai an samu matsalar. Idan ƙasashen da suka cigaba suka yi kiɗa, mu kuma sai mu yi rawa, ka san da haka, ni ma na sani.

Yaƙin Yukiren da Rasha yana da tasiri sosai a kan tattalin arzikin ƙasarmu da ma ƙasashen da suka fi ta a fuskar tattalin arziki. Me ya sa za mu tsuke tunaninmu a iya zancen abubuwan da ba a yi ba?

Tsofaffin takwarorinka a majalisar ƙasa sun yi iƙirarin tsige shugaba Buhari matuƙar bai yi wani abu a kan matsalar tsaro ba a cikin lokacin ds suka ɗebar masa. Wannan abin ya dame ka, ko kuma wasan yara kawai ka ɗauki abun? 
A matsayina na shugaban jam’iyyar dole abin ya dame ni a lokacin da na ji. Amma faɗar abu daban, aikata shi ma daban. Na san wani salo ne daga mutanen da ba su samu biyan buƙatarsu ba ne. Suna son su yi amfani da matsin lambar da ‘yan adawa suka yi. Wasu ma sun zaƙe sosai don a saurare su. Kuma komai ya dawo kunnenmu. 

Ko su ne mambobin da suka faɗi takara a zaɓen fidda gwani?  
Bana son kama suna a nan. Amma su ne a kan gaba-gaba. Sun goya wa ‘yan adawa baya, kuma sun ɗora wa jam’iyya da gwamnati laifi. 

Za ku ɗauki wani mataki a kansu?
A’a, ba dole ba ne. Komai muna yi masa abinda ya dace da shi. Ni na fi jin haushin ma abin da wasu ministocin suka yi a kan ‘yan majalisar. Tunda su zaɓar su aka yi kuma suna da ‘yanci, wanda nake girmamawa. Ni ma na taɓa aiki tare da su, kuma na san halin da suke ciki. Ina girmama ra’ayoyinsu, amma na san komai zai wuce da yardar Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *