Za mu kawo sauyin da zai bunƙasa rubutun adabi – Bala Anas Babinlata

“Da yawa masu aibata rubutun Hausa ba sa karanta littafan”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuci Malam Bala Anas Babinlata ba voyayye ba ne a fagen rubutun adabi da shirya finafinan Hausa. Littafinsa na ‘Ɗa Ko Jika’ na daga cikin ayyukansa da suka ƙara masa ɗaukaka da shuhura a duniyar adabi, saboda irin salon rubutunsa mai tafiya da tunanin mai karatu, musamman a tsakanin shekarun 1991 zuwa 2000. A tsakanin wannan lokaci Bala Babinlata ya rubuta littattafai har fiye da 10, waɗanda akasarinsu sun shiga gidaje da dama a Nijeriya har da ƙasashen waje, wasu kuma an karanta su a tashoshin gidajen rediyo daban-daban. Kodayake bayan tsawon lokaci masu karatu sun daina jin ɗuriyar marubucin wataqila sakamakon sauya sheƙa da ya yi zuwa harkar fim, wacce ta janye shi daga kusan duk harkokin sa har da aikin da ya ke yi na gwamnati, don ba da haƙƙin abin da ake so, kasancewar sa mutum ne mai kiyaye ƙa’idojin aiki da bin tsari. Yanzu haka Bala Babinlata da haɗin gwiwar wasu masu kishin cigaban harkokin rubutun adabi, sun duƙufa, domin samar da wani tsari da zai ceto harkar rubutun littattafan Hausa na da da na yanzu, tare da share hawayen marubuta da su ke ganin ’ýan kasuwa na ci da guminsu. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya gana da fitaccen marubucin Hausan, don jin inda ya ɓuya da kuma aikin da yake yi da mutanen ɓoye!

MANHAJA: Mu fara da sanin waye Babinlata?
BABINLATA: Sunana Bala Anas Babinlata. Haifaffen Kano ne ni. Bayan kammala karatuna na ɗan yi kasuwanci na ɗan gajeren lokaci kafin na fara aiki a ma’aikatar yaɗa labarai a shekarar 1991. Na fara rubutu a shekarar 1980, amma ban fara buga littafi ba sai a shekarar 1991, wato shekarar da na fara aiki kenan. A shekarar 1995 na bar aiki don ra’ayin kaina na mayar da hankali a kan rubutu da shirin fim. Na halarci bitoci a kan shirin fim a wurare daban daban irin su Abuja, Legas da New Delhi da ke Ƙasar Indiya. Na yi aure a shekarar 1997, kuma yanzu haka ina da ‘ya’ya biyar, uku mata da maza biyu.

Daga ina wannan suna na Babinlata ya samo asali?
Sunana ne da na matata.

Wacce gwagwarmaya aka sha lokacin karatu, yaya ya kasance?
Ban yi wata doguwar gwagwarmaya a fagen karatu ba. Tun da a lokacin babu wani babban ƙalubale game da karatu. Ba irin yanzu ba da dole mutum yana buƙatar manyan digiri kafin ya kai labari a rayuwa. ‘Professional certificate” kawai na yi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, wato Kano State Polytechnic. Kuma ban jima da gamawa ba na samu aiki. Sai dai bayan da na shiga harkar fim na lura da ƙalubalen sana’a ce mai buqatar ilimi sosai, amma karatunta a lokacin dole sai an fita ƙasashen waje, ga shi ba ni da kuɗin fita waje a lokacin. Saboda haka da yake akwai yanar gizo a lokacin sai na nemi wata makarantar yanar gizo dake Amurka mai suna Film School Online, sai dai ba sa karvar ɗaliban da ba a Amurka suke da zama ba. Don haka sai na tuntuɓi Farfesa Abdallah Uba Adamu ya haɗa ni da wani amininsa Malam Salisu Ɗanyaro wanda ke zaune a Jihar New Jersey dake Amurka, ya yi min rijista ta adireshinsa. Matsalar dai ita ce ba zan samu satifiket ba tun da ba a can nake ba, amma dama ni ba satifiket ne ya dame ni ba, tun da ba aiki zan nema ba, ilimin kawai nake buƙata. Karatun da na yi a wannan makaranta ta yanar gizo ya buɗe min ƙwaƙwalwa sosai game da yadda ake yin fim. Daga nan sai na mayar da hankali a fagen bincike a yanar gizo game da rubutu da shirin fim.

Kana cikin matasan marubuta da suka yi shuhura a shekarun baya, ba mu labarin yadda ka samu kan ka a matsayin marubuci?
Shahara a rubutu tana da bambanci da shahara a fim. Saboda marubuci yana haɗuwa da makaranta ba su ma san marubuci ne kai ba. Wasu su yabi rubutun ka wasu su soke ka. Wanda hakan ya kan baka damar ka ji kurakuranka daga bakin mutane. Savanin tauraron fim wanda duk in da aka ganshi an gane shi. Wasu abokaina suka riqa nuna damuwa wai idan suka ce sun sanni ana ƙaryata su. Sai na yi dariya na ce, “nima idan na ce na sanni wasu ƙaryata ni suke yi.” 
Babu abu mafi daɗi a rubutu irin yadda kake rubuta labari ya yi tasiri a rayuwar mutane. Har yanzu ina tuna wani bawan Allah ya taɓa yin gadi a kamfanin siminti na Ashaka, da ya taɓa rubuto min wasiƙa, lokacin babu wayar hannu, yana gode min. Ya ce, bai iya karatu ba, bai iya rubutu ba, idan zai aika da wasiƙa gida sai an rubuta masa, haka nan idan aka rubuto masa amsa. Amma ta dalilin littafin ‘Ɗa Ko Jika?’ da ake karanta wa a rediyo ya dage ya koyi karatu don ya karanta da kansa maimakon ya jira a rediyo.


Haka nan littafina na ‘Zinaru’ ya tayar da ƙura sosai. Ban zaci zai yi tasiri mai yawa irin yadda ya yi ba. Har kotu an gayyaci Marigayi Mustapha Gangara shaida, (Allah Ya jikansa da gafara) shi ke karanta littattafai a shirin Shafa Labari Shuni na Rediyon Tarayya na Kaduna a lokacin. Yawancin mutane suna yin mamakin wai mai ya sa mun shahara a rubutu amma ba mu yi kuɗi ba? Shi rubutun Hausa ana yi ne don sha’awa kawai.

Littattafai nawa ka rubuta kuma ka wallafa?
Littattafai goma sha uku na wallafa. Amma akwai da dama da na rubuta, amma ban wallafa su ba. Daga ciki akwai ‘Kulu’, ‘In Da Alƙawarin’, ‘Maji Ma Gani’, ‘Sihirtacce’, ‘Ɗa Ko Jika’, ‘Mubarak’, ‘Zinaru’, ‘Ƙwarya Tagari’, ‘An Yanka Ta Tashi’, ‘Tsuntsu Mai Wayo’, ‘Sara Da Sassaƙa’, ‘Rashin Sani da Rubutun Fim’. 

Ana ganin sunanka a cikin wasu finafinai na Hausa. Shin daga rubutu ne aka koma shirya fim?
Asalina ɗan wasan kwaikwayo ne tun kafin na fara buga littafi, amma gaskiya a rubutu na fi shahara.

Akwai littafin da ka wallafa mai suna ‘Rubutun Fim’. Menene manufar ka ta rubuta wannan littafin?
Tun a farkon lokacin da muka fara film a 1990 har muka shekara sama da goma muna rubutun fim muna yi ne a zubin labari kamar dai yadda muka saba a littafi. Fim yana da bambanci da littafi. Duk abin da za ka rubuta a littafi komai gundurar mai karatu da ya yi bai hana makaranci ya haƙura ya karanta har sai ya kai ƙarshe. Saɓanin fim, masu kallon film mutane ne masu gajen haquri ainun. ‘Yar ƙaramar dama suke so ka ba su su tura fim ɗin ka gaba, wasu ma su tashi su yi tafiyarsu su qyale fim ɗin, ba Bahaushe kaɗai ke da wannan ɗabi’ar ba, ɗabi’ar mai kallo ce a duk duniya. Dalilin da ya sanya aka ƙirƙiri tsarin yadda ake jera labarin fim ta hanyar da ba zai taɓa gundurar mai kallo ba daga farkon sa har zuwa ƙarshe.

Wannan ne dalilin da ya sa na yi littafin ‘Rubutun Fim’ littafi ne da aka tanade shi don ya zamarwa marubuci musamman na fim jagora yayin sarrafa labarinsa zuwa labarin fim. Babu wani salo na fim da littafin bai taɓa ba. Haka nan littafin yana gwadawa marubuci cewa duk abin da yake so ya rubuta to, wani tuni ya rubuta irinsa a baya, wannan zai bai wa marubucin damar ya yi nazarin waɗanne labarai ne aka yi irin nasa a baya, kuma mai zai yi ya kauce wa sauran da aka yi kafin nasa. Littafi ne da ya farfasa gaɓoɓin labari daki-daki, ta yadda marubuci zai gane kowacce gava takamaimai mai take buƙata ba tare da ya wahalar da kansa ba.

Duk da irin ɗaukakar da ka samu a baya, daga bisani an ji ka shiru a fagen adabi. Shin kai ma ka ajiye alƙalamin ne?
Shi alƙalami ba a ajiye shi. Kullum marubuci da tunanin rubutu yake kwanciya yake tashi. Kamar yadda na faɗa maka a baya ba kuɗi ke riƙe da marubuta ba, a harkar rubutu sha’awa ce. Sai kuma muka yi rashin sa’a Bahaushe suka ya gwanance da shi ba yabo ko ƙarfafa gwiwa ba. Duk abin da marubuci zai rubuta komai nagartarsa sunansa ɓata tarbiyya a wajen al’umma. Abin takaici yawancin masu tsine maka ko shafi ɗaya ba sa karanta wa, amma su ne gwanayen suka, su ne ma al’umma ke jinjina wa. Wannan ne dalilin da ya sa zai yi wuya marubuci ya girma da rubutunsa, saboda waɗanda kake yi domin su basa yabawa. Ka ga kenan rubutu zai daɗe bai bunƙasa ba, saboda idan ka ajiye alƙalaminka dole wasu su taso su gaje ka. Yaran da za su gaje ka, ba su san komai ba, daga rayuwar makaranta sai hulɗarsa da budurwarsa ba zai yi tsalle ya wuce tsayinsa ba. Kafin shi ma suka ya kore shi tun kan ya girma. Ko su Dr. Abubakar Imam sun girma da rubutun su ne saboda tallafa wa da kulawa da NORLA da NNPC suka ba su.

A ganin ka menene ya haifar da durƙushewar harkar rubutun adabi irin wanda kuke yi na littafi?
Abubuwa ne da dama suka durƙusar da rubutu. Daga ciki akwai mafi girma wato rashin tsari. Na biyu shi ne guguwar Yanar Gizo da ta zo ta tashi sana’o’i da yawa daga aiki. Amma dai ko ita ɗin ma rashin tsarin ne dai ya haifar da matsalar da aka samu. Idan na ce rashin tsari ya haɗa da abubuwa da yawa. Da farko dai gaba ɗayan mu mun zama mawallafa ne saboda gazawar kamfunan talifi irin su NNPC da Al-Huda-Huda da makamantansu da suka kasa buga littattafan marubuta saboda sun raina ribar da ake samu, wanda hakan ya shigo da mu harkar ɗab’i muka shigo muka yi ta buga littattafan mu da kan mu. 
Matsalar ita ce, Bahaushe bai ganewa duk kasuwancin da za a ce na haɗaka ne ba. Mun fi gane tuwona-maina. Hakan ya sa ba mu iya kafa kamfuna masu ƙarfi da za su iya ɗorewa ba. Wannan ya bai wa dillallan sayar da littattafan damar ƙwace harkar. Su fa waɗannan dillallan marubuta ne suka tara musu kafin da suke yaƙarsu, saboda ai kayan bashi ake ba su sai sun sayar su biya a tsittsinke. Su ma kuma daga ƙarshe yanar gizo ta zo ta kore su.

Harkar rubutu da rayuwar marubuta ta koma yanar gizo, menene ra’ayin ka kan wannan sabon tsari?
Ko da yake dai akwai matsalar satar fasaha, amma za mu iya cewa cigaba ne sosai ga marubuta idan suka nutsu suka fito da hanyar da za su ci gajiyar abin. Na farko dai wallafa ta qara sauqi tun da ba lallai sai marubuci yana da kuɗin buga littafi zai yi wallafa ba. Sannan waya ta sauƙaƙa abubuwa da dama. Duk mai neman littattafan ka yana iya tuntuvar ka ta waya ko ta WhatsApp ya yi maka ciniki ba lallai sai ya shiga kasuwa ba. Matsalar ɗaya ce yadda yanar gizo ta zama hanyar sakin littafi ba tare da dubawa ko shawarwarin ƙwararru ba.

Wacce gudunmawa kake ganin za ku bayar domin farfaɗo da harkar rubutu da kasuwancin littattafai?
Akwai hanyoyin kasuwanci da dama a yanar gizo, daga cikin waɗannan hanyoyi mun dubi waɗanda suka kasance mafi sauƙi don farfaɗo da kasuwar littattafai da ma adana su. Mafi tashin hankali a cikin sha’anin littattafan mu shi ne ɓacewar littattafan mu daga doron ƙasa tun muna raye. Wannan ba ƙaramin ƙalubale ba ne.
Bayan tsawon lokaci muna nazari a kan yadda kasuwancin littattafai ya taɓarɓare mun gano makaranta da dama sun koma karatu a yanar gizo, haka nan akwai makaranta masu tarin yawa waɗanda su har yanzu burin su su karanta littafi bugagge a takarda. Saboda haka ni da wani marubuci abokina Ɗanladi Haruna muka fidda taswirar wata manhaja da za ta haɗa makaranta da marubuta, ta yadda makaranta za su iya neman duk littafin marubucin da suke so, ko da ya ɓata. Manhajar tana da tsarin yadda za ta haɗa kai da marubucin su nemo littafin a sake buga shi duk a cikin manhajar, don mabuƙata su samu. Makaranci zai iya sayen littafi na yanar gizo ko bugagge kai tsaye daga manhajarmu, a kuma cire wa mai littafin ribarsa ba tare da ya sanya ko kwabonsa ba. Shi kansa marubuci yana da ‘yanci ya tsara wanne nau’i na littafi ya amince a saya daga gare shi. Na yanar gizo ko bugagge? Daga ƙarshe bugu da aika littafi duk aikin manhajarmu ne. Wannan zai taimaka sosai musamman a wannan zamanin da littafi kwafi dubu ke da wuyar bugawa.

Yaya kake hasashen wannan harka ta rubuce rubucen littattafan Hausa za ta kasance nan da wasu shekaru masu zuwa?
Idan muka yi abin da ya dace zamu iya farfaɗo da harkar rubutu har ta ninninka da, saboda kasuwar yanar gizo kasuwa ce ta duniya ba kamar ƙananan kasuwannin mu da muka saba a baya ba. Yau za ka saki sabon littafi za a saye shi daga ko’ina a lokaci ɗaya. Ga hanyoyin tallata haja kullum ƙara daɗuwa suke yi savanin da, da ko tallan ma ba ma yi.

Wanne tallafi da goyon baya matasan marubuta masu tasowa za su samu daga wajenku?
Ai wannan manhajar waɗanda za su fi morar ta matasa ne. Ita za ta kawo ƙarshen gorin da ake yiwa ‘online writers’ na cewa ba su da bugaggen littafi. Saboda za a buga littafinsu ga masu buƙata a takarda.

Menene shawarar ka ga matasan mata marubuta da suka ƙwace ragamar harkar rubutu a halin yanzu?
Ba ragamar rubutu mata suka ƙwace ba, yanayin kasuwar littafi ta shiga a baya ne ya bai wa mata dama, lokacin da dillallan littafi suka kassara marubuta maza suka karya tattalin arziƙin su na buga littafi, a lokacin sai mata suka rinqa buga littafi fiye da maza har littattafan su suka mamaye kasuwa. Amma yanzu labarin ya sauya ai. Tun da kasuwar ta mutu gabaɗaya. Amma duk da haka ƙalubalen da ke kan marubuta maza shi ne babu wadatar bincike da zurfafa tunani a littattafan su. Yayin da mata suka zuƙe suka koma ba sa rubuta komai sai matsalar kishiya kamar ita kaɗai ce matsalar al’umma. A ƙarshe ina kira ga matasa maza da mata da su sake zabura su kaifafa alƙalumansu don samar da rubutu mai nagarta.

Shin kana cikin wata ƙungiyar marubuta ne?
Ina cikin duk ƙungiyoyin marubuta daban daban, amma a matsayin uba mai bayar da shawara.

Wacce harka ce ta fi ɗaukar hankalin ka a harkokin ka na yanzu?
Harkar shirin fim ta fi ɗaukar hankalina da lokacina fiye da komai a yanzu.

Wacce karin magana ce ta fi tasiri a rayuwarka?
Kowa daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.

Mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *