Za mu koma Ukraine idan yaƙi ya lafa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Mamaye Ukraine da Rasha ta yi ba wani sabon labari ba ne a ’yan kwanakin nan. Kazalika, batun ƙasashe na jigilar jama’arsu da ke Ukraine shi ma labari ne da duk mai bibiyar labaru ya san an yi haka ko a na cigaba da yin hakan. Abin takaicin shi ne yadda ’yan Afirka ko a ce baƙaƙen fata su ka fuskanci ƙalaubalen nuna mu su wariya wajen isa tudun mun tsira daga tsakiyar inda a ke fargabar saukar makamai masu linzami zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da Ukraine. Wasu daga ɗaliban Nijeriya sun ba da tabbacin samun cikas wajen kulawa da su a wajen yunƙurin ficewa daga Ukarine.

Kasancewarsu baƙaƙen fata a kan maida su can baya a layi inda wasu su ka share lokaci mai tsawo cikin sanyi kafin samun nasarar ƙetarawa. Ma’aikatar wajen Nijeriya ta bakin ƙaramin minister Ambasada Zubairu Dada ya nuna damuwar Nijeriya kan haka da ma tabbatar da cewa gwamnati ta isar da ƙorafin inda ya dace don sanin matsayar Nijeriya.

Da farkon lamarin babban ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya buƙaci kar ’yan Nijeriya da ke Ukraine su tada hankalin su don ƙasar Rasha sassan da farar hula su ke ta ke kai harin ba. Koma dai ya za a ce akwai tsananin zullumi a Ukraine kuma hatta wasu ’yan ƙasar da ba sa shirin arcewa na riƙe da bindiga da zummar kare ƙasar su. Kuma ko a yanzu haka ƙasar ta gabashin Turai ba ta barin matasa da su ka dace da yin aikin soja su fice, ta kan buƙace su, su dakata don kare ƙasar su.

Haƙiƙa wannan babban yaƙi ne amma ba da zummar kashe fararen hula ba sai don mamaya. Don a gaskiya inda yaƙin hallaka jama’a ne da tuni an kammala wannan yaƙin. Duk da haka an samu asarar rayuka. Duk da ƙarfin Rasha ta ba da labari da kan ta na rasa ran aƙalla sojoji 500 ga kuma waɗanda su ka samu raunuka. Ga wanda bai fahimci yaƙin ba a takaice dai tsama ce da ke tsakanin gabashin turai da yammacin Turai, ko a ce tsakanin ƙasar Rasha mai ƙarfin makamai da tasiri tun daga zamanin tsohuwar daular SOBIYET da kuma yammacin Turai musamman Amurka.

Bayanai na nuna Rasha na rigakafin hana yammacin Turai amfani da Ukraine da ke maƙwabtaka wajen jibge makamai da hakan a ƙarshe ka iya barazana ga tsaron ɗaya daga manyan daulolin na duniya. Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ba haka ya ke ɗaukar lamarin ba kuma ya fi ƙaunar ƙasarsa ta ƙulla ƙawance da yammacin maimakon Rasha. Zelensky na yunƙurin Ukraine ta samu shiga ƙungiyar tarayyar Turai kamar yadda Turkiyya ke ta wannan gwagwarmaya tsawon zamani.

Hakanan Zelensky na son ƙasarsa ta samu zama memba ta ƙungiyar tsaron yammacin Turai wato NATO maimakon gabashin Turai wato Warsaw. Shugaban Rasha wanda tsohon jami’in sirri ne ya daɗe da fahimtar wannan ƙalubale don haka ba zai ɗauki hakan da wasa ba. Ko da za a kushe Rasha da mamaye Ukraine to ba za a yi mamaki ba don yadda manyan ƙasashen duniya mafi ƙarfin makaman NUKILIYA kan yi hamayya da juna da maida wasu ƙananan fagen gwada ƙarfin makaman su da siyasar su ko ma muradun su. Babban misali ma a nan it ace ƙasar Sham inda Rasha ko ruwan boma-bomai don kare gwamnatin Bashar Al’Asad yayin da Amurka ke kare muradun ’yan hamayya.

Kar mu yi nisa ba mu tavo takunkumi daban-daban na ƙasashen yammacin Turai da ƙawayen su ke aza wa Rasha don mamaye Ukraine. Kai kuwa irin waɗannan takunkumi na zaman madadin yaƙi ne don manyan ƙasashe na shakkar yin yaƙi da juna tun bayan yaƙin duniya na biyu da madugun ’yan Nazi wato Adolf Hitler na Jamus ya haddasa. Abun fahimta a nan me ya faru da Iraqi lokacin da ta mamaye Kuwait? ai nan ta ke manyan ƙasashe har ma da ƙanana su ka yi taron dangi su ka riƙa ruwan wuta har sai da su ka fitar da sojojin marigayi Saddam Hussein daga ƙasar.

Wannan ma shi ya ƙara harzuƙar silar cewa Saddam na makamai masu mummunar ɓarna don haka daga bisani a ka sake ƙaddamar da yaƙi kan Iraƙi har a ka kifar da gwamnatin ƙasar. Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu Iraƙi ba ta dawo daidai ba. Yanzu me zai hana ƙasashe su ƙara shiri don aukawa Rasha su fitar da ita daga Ukraine? Iya dai matakin na karya tattalin arziki ne da cacar baki.

Gaskiya ba wai don ƙasashen yammacin turai na tsoron Rasha ba ne a’a ba buƙatar yaƙin ne ko ba ribar da za a cimma. Kazalika za a yi rugu-rugu ne da zai iya kifar da ƙasashen duniya da dama. Wannan ma ka iya zama yaƙin duniya na uku.

Mu dawo batun jigilar ’yan ƙasashen Afirka da ma musamman Nijeriya daga Ukraine. Tuni an ɗauki kamfanonin jirage biyu baya ga ware dala miliyan 8.5 don ɗawainiyar kwaso waɗanda su ka maqale da akasarin su ɗalibai ne. An samu nasarar wasu da dama daga ɗaliban sun ratsa iyaka da samun mafaka a ƙasashen makwabtakan Ukraine irin su Romania, Poland, Slovakia da Hungary.

Wasu daga iyayen yara da su ka taru a filin saukar jiragen sama na Abuja don tarbar ’ya’yan su da a ka kwaso daga Romania, na nuna kwarin gwiwa cewa da zarar fitinar Ukraine ta lafa za su sake maida ’ya’yan su. Iyayen ba sa raba ɗaya biyu na haramar sake tura ’ya’yan su ƙasar ta gabashin turai da zarar yaƙi ya lafa. Wannan na nuna sun ji sun gani kuma sun amince cewa yaran su na samun ilimi mai inganci da watarana za su dawo gida don ba da ta su gudunmawa.

Iyayen na magana ne a lokacin da jirgi na farko ɗauke da ɗalibai kimanin 415 na kamfanin MAX ya sauka ɗauke da ɗaliban maza da mata. Akwai alamun gajiya a jikin ɗaliban da kuma ajiyar zuciya don isowa tudun mun tsira bayan galabaita wajen ficewa daga Ukraine zuwa Ramania da ke makwabta ka.

Ɗaya daga iyayen Jibrin Muhammad ya ce, ai ba za a ki maida yara makaranta ba da zarar lamura sun lafa. Mahaifin yaro Yusuf ya ƙara da cewa ba za su so barin ‘ya’yan su a jami’o’in Nijeriya inda a ke samun cikas ta wajen tafiya yajin aiki ba ƙaƙƙautawa ba.

Mata da ke cikin ɗaliban na nuna auna arziki da murnar gamuwa da iyayen su bayan fama da gallafiri tsakanin ɗaliban sauran ƙasashe da ke karatu a Ukraine. Matan sun nuna ƙorafin yadda a ka riƙa mayar da su baya can a kan layin ƙetara Ukraine duk da an ɗauki matakin fara ba wa mata dama, amma kasancewar su baƙar fata sun sha takaicin nuna mu su wariya. Ba ma wannan kaɗai ne matsalar ba, duk lokacin da ɗan ƙasar Ukraine ya zo arcewa, a kan buda ma sa hanya ya shiga gaba maimakon a riƙa ɗaukar duk jama’a ɗaya ne.

Jami’in labarun kamfanin jiragen sama na MAX Ibrahim Dahiru da ya fara dawo da ɗaliban ya ce, iya sawun farkon kawai a ka ba shi umurni don haka za a jira a sake shirya wasu ɗaliban don sake kwaso su.

Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta ce baya ga ɗalibai 5000 da a ke da alƙaluman su, akwai wasu mutane da ke aiki ko kasuwanci da su ka fi dubu 2000 da ke ƙasar ta Ukraine. Hakanan ma’aikatar ta ce, ba lalle sai an dawo da wanda ba ya sha’awar dawowa ba. Ƙaramin ministan waje Zubairu Dada ya ce akwai ’yan NIjeriya da ba su shirya dawowa ba, don haka ba za a tilasta su, su dawo ba matuƙar ƙasashen da su ke fake za su ƙyale su, su zauna har a samu kwantawar ƙura.

In mun koma kan fitinar ƙungiyar tsaron yammacin Turai NATO ta ƙi amincewa da buƙatar ƙasar Ukraine ta ayyana sassan gewayen Ukraine a matsayin inda a ka haramta tashin jirage. Ƙasar Ukraine da asalin ta yankin tsohuwar tarayyar SOBIYET ne da ke da helkwata a Masko na Rasha, na buƙatar shiga ƙungiyar tarayyar yammacin Turai da rejista da NATO, amma zuwa yanzu ba ta cimma muradun biyu ba.

Babbar sakataren NATO Jens Stoltenberg ya ce hana tashin jiragen zai ƙara ta’azzara yaƙin ne da ƙara girman sa a Turai, amma gara yanzu da ya tsaya kan Rasha a matsayin ta kai harin mamaya ga makwabciyar ta.
Stoltenberg ya ce NATO za ta cigaba da ba da tallafi amma ba kai tsaye irin na hana jirage tashi ba.

Burin Ukraine na hana jirage tashi shi ne don dakatar da jiragen yaƙin Rasha daga ketawa samaniyar Ukraine da kewaye, da har dai hakan ma zai yi tasiri sai ya zama wajibi NATO ta fito da sojoji ko ta yi yunƙurin harbo jirgin Rasha da ya saɓa umurnin, inda ita kuma Rashar za ta maida martani. Shi kuma martanin na nuna yaƙi ya rincabe fiye da ƙasashe biyu zuwa manyan ƙasashen duniya.

Tuni shugaban Rasha Vladimir Putin ya umurci jami’an sarrafa kunamar makamin Nukiliya na ƙare dangi su zauna cikin shirin ko-ta-kwana. Allah ya tsayar nan!