Za mu magance matsalar cin zarafin mata a hidimar ƙasa – Daraktan NYSC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Darakta Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) Brig Gen. Yushau Ahmed, ya ce za su magance matsalar cin zarafin mata a NYSC.

Babban daraktan wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin gangamin wayar da kan al’ummar karkara a Bauchi, ya ce shirin ya dade yana yaqi da GBV ta hannun ƙungiyar ta Corps Gender Vanguards.

Darakta Janar na hukumar ta NYSC a Jihar Bauchi, Misis Rifkatu Yakubu, ta wakilce shi, ta bayyana cewa, an samar wa Vanguards kayayyakin aikin da suka dace don gudanar da gangamin wayar da kan jama’a da ayyukan tallafi a yankunan karkara.

Ahmed, wanda ya bayyana cewa shirin wayar da kan jama’a yana gudana ne a lokaci guda a duk jihohin Arewa, ya bayyana cewa, jami’an tsaro sun kuma taimaka wajen samar da ƙungiyoyin jinsi a makarantu.

A cewarsa, waɗannan ƙungiyoyin kula da jinsi sun samu damar samar da hanyoyin sadarwa ga waɗanda aka ci zarafinsu ta hanyar layin kyauta na GBV, 08031230651, wanda ma’aikatar mata ta tarayya ta samar.

Ya kuma bada tabbacin cewa NYSC za ta ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin samun nasarar daidaita jinsi a ƙasar nan, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tallafa wa hukumar ta NYSC Gender Vanguard ta hanyar samar da yanayi mai kyau da zai yi tasiri.

Yayin da ake yawan yin kuskuren la’akari da batutuwan da suka shafi jinsi suna shafar mata ne kawai, yana da muhimmanci a nuna cewa sun haɗa da abubuwan da suka shafi jinsi biyu, gami da haƙƙoƙi da nauyi.

“Wannan ya sanar da zaɓin taken Daidaiton Jinsi, Mutunta kowa da kowa kuma yana da muhimmanci a tunatar da kowa da kowa cewa GBV ba kawai ta jiki da tunani ba ne amma har ma ta ƙunshi cin zarafin ainihin haƙƙin ɗan adam na waɗanda abin ya shafa.

Alh. Aminu Ibrahim mataimakin daraktan aikewa da matsuguni na NYSC Bauchi ya yaba wa mahukuntan NYSC bisa yadda suke kishin al’amuran da suka shafi rashin daidaito tsakanin maza da mata wanda ya sanya aka gudanar da wayar da kan jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *