Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar makiyaya a Nijeriya ta Miyetti Allah (MACBAN), ta ce ta ɓullo da dabarun daƙile ƙalubalen tsaro da ke addabar makiyaya.
A cikin wata sanarwar da ta fitar a Abuja cikin makon nan, ta ce waɗannan dabarun sune sakamakon taron da majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ta gudanar.
Sanarwar ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar ta MACBAN na ƙasa, Alhaji Hussein Bosso da sakataren ƙasa, Baba Ngelzarma.
Ya bayyana cewa, taron ya tattauna ne kan ƙalubalen tsaro da makiyaya ke fuskanta a faɗin ƙasar da kuma batutuwan da suka shafi zavukan ƙasa na MACBAN mai zuwa.
Har ila yau, ya bayyana cewa, MACBAN za ta bai wa gwamnati da jami’an tsaro cikakken goyon baya don magance ’yan fashi da makami, da ’yan bindiga da sauran miyagun laifuka da ke sa rayukan makiyaya cikin haɗari a yankunan karkara.
Ya bayyana cewa, hukumar zaɓe ta umurci sassan jihohi da su gudanar da tarurruka na gari, waɗanda suka haɗa da shugabanni, shugabannin matasa da sauran masu ruwa da tsaki don magance wasu matsaloli na musamman da ke yaƙi da ilimin makiyaya.
“An kuma umarci sassan jihohin don magance matsalolin da ke shafar rayuwar makiyaya da kuma yin kira ga al’adun ‘Pulaku’ a kan duk wani iyali da ke da hannu ko kuma ke taimaka wa aikata laifuka.
“Ƙungiyar ta bayyana jin daɗinta da irin tallafin da ta samu da kuma damuwar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III kan halin da makiyaya ke ciki.
“MACBAN na tabbatar wa Sarkin cewa, ƙungiyar za ta yi duk abin da ya kamata don dawo da martaba, al’adun Fulani da kuma magance matsalolin da suka shafi makiyaya da duk abin da ya dace,” inji ta.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta yi kira ga Sarkin Musulmi da ya shirya taron ƙasa wanda ya haɗa da shugabannin makiyaya da masu hankali da sauran masu ruwa da tsaki.
“Wannan na da nufin magance matsalolin rashin tsaro, ƙarfafa tattalin arziki da kuma haramta munanan kalamai na makiyaya a kafafen sada zumunta da na zamani.
“Taron ya kuma nuna matuƙar damuwarsa kan yadda dubban iyalan makiyaya ke cigaba da ƙaurace wa gidajensu sakamakon satar shanu, ’yan bindiga, garkuwa da mutane da ayyukan haramtattun laifuka.
“Suna kai hari, su raunata, ko kuma kashe makiyaya ba tare da wani dalili ba. Idan aka cigaba da hakan nan ba da jimawa ba za a iya durƙusar da harkar kiwo baki ɗaya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, taron ya amince da bin ƙa’ida, dokoki da ƙa’idojin gudanar da zavukan ƙasa na MACBAN mai zuwa.
Taron na NEC wanda shugaban ƙungiyar MACBAN ya jagoranta ya samu halartar shugabanni da sakatarorin tarayya na jihohi 36 na tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa, ‘Ardo’ (Shugaban Ruga) na ɗaya daga kowace jiha da wakilan Sarkin Musulmi, Sarkin Kano, Sarkin Zazzau (jihar Kaduna) da Sarkin Katsina sun halarci taron.