Za mu samu kason ƙuri’un da muke buƙata a Kudu maso Gabas – Shugaban APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa, jam’iyyar na sa ran samun sama da kashi 25 na ƙuri’un ’yan yankin Kudu maso Gabas.

Ya yi magana ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da kwamitin sulhu na mutane takwas a jihar Abia ƙarƙashin jagorancin Sanata Chris Adighije.

Adamu ya buƙaci shugabannin shiyyar da su tashi tsaye wajen kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su kuma yi ƙoƙarin ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zaɓe.

Ya ce, “Bari Abia su je su daidai tare. Duk zavukan ƙasa – ‘yan majalisar wakilai, dattijai, na gwamna, zaɓen shugaban ƙasa – ba za mu gamsu da kashi 25 na ƙuri’un da aka kaɗa ba.

“Muna buƙatar mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa wa APC. Babu rabi game da shi. Idan za mu ci nasara, dole ne mu yi ƙoƙari mu ci kowace jiha.

“Dole ne mu yi wasu ayyuka kuma mu tsaya tare. Wannan shi ne lokacin da za a haɗa kai; wannan shi ne lokacin da za a yi aiki don haɗin kai. Idan muka yi haka, Allah zai kasance tare da mu.”

Adamu ya shawarci ɓangarorin da ke rikici da juna a Abia da su ajiye banbancinsu kuma su yi aiki domin samun nasarar jam’iyyar.

“Ina fatan da abin da muka yi na ƙaddamar da kwamitin zai sa a samu zaman lafiya kuma muna fatan wannan shi ne mataki na ƙarshe. Ba za mu sake yin taron sulhu ba.

“Yanzu za mu bar wa shugabannin Abia su je su yi siyasarsu a jihar Abia. Siyasa ta cikin gida ce,” Adamu ya shaida wa ɓangarorin.

Sanata Adighije ya yi alƙawarin yin aiki domin haɗa kan jam’iyyar a jihar.

Ya ce, “muna kan hanyarmu ta komawa Abia ne domin mu taka rawar gani a siyasar cikin gida, mu sasanta dukkan ’ya’yanmu da kuma tabbatar da cewa mun tafi kai tsaye wajen neman nasara.

“Na san cewa da yardar Allah da kuma tare da tawagar, za mu yi abin da ake buƙata da kuma tabbatar da nasara ga jam’iyyarmu.”

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da mataimakin babban mai shigar da ƙara na majalisar wakilai, Nkeiruka Onyejeocha (Sakatare); Ƙaramin Ministan Kimiyya, fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Cif Henry Ikoh; tsohon Ministan Ƙwadago da Ƙarfafawa, Dr Emeka Wogu; Sakataren walwala na jam’iyyar APC na ƙasa, Sir F.N. Nwosu; ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Abia, Chief Ikechi Emenike, da tsoffin ’yan majalisa Emeka Atuma da Martins Azubuike.