Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya sanar da aniyar Gwamnatin Tarayya na sanya Nijeriya ɗaya daga cikin ƙasashe 80 masu gina ɗan adam ta hanyar samar da inganci a ɓangarori da dama.
Shettima a bayyana hakan ne a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, a lokacin da ya ke ƙaddamar da tsarin gina ɗan adam na kwamitin ci-gaban shirin gina ɗan adam a ranar Juma’a.
Ya ce, su na da burin cimma hakan nan da shekarar 2030 don tabbatar da canza tsarin rayukan al’umma da inganta hanyoyin samun ingantacciyar lafiya, ilimi, faɗaɗa damammakin ayyuka da samar da yanayi mai ƙarfi ga ƙalubalen harkokin duniya.
Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda a shekarar 2018 Nijeriya ta kasance a mataki na baya ta fuskar lafiya, ilimi da kuma ɗaukar aiki.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnati ta shirya tsaf don ganin ta cimma nasarar a fannonin nan da 2030.
A lokacin da ta ke jawabi a taron, Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan Majalisar Tattalin Arziƙi (NEC) da Suayin Yanayi, Rukaiya El-Rufa’i ta ce shirin zai mayar da hankali ne kan ɓangarorin Ilimi, Lafiya da Ci-gaban ayyukan yi.
Ta bayyana muhimmancin yin nazari da sanya ido kan shirin don tabbatar da nasara ga ababen da ake da burin cimma wa.