Za mu tabbatar da tsaro a Kano da kewaye yayin zaɓe mai zuwa – CP Gumel

Daga RABIU SANUSI a Kano

Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano da zai kula da aikin zaɓe mai zuwa a jihar, CP Usaini Mohammed Gumel, ya bada tabbacin cewa za su sa ido matuƙa tare da ɗaukar matakan dasuka dace wajen ganin an gudanar da sahihin zaɓe a jihar.

CP Gumel ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis a karon farko a matsayin Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, inda zai jagoranci hidimar zaɓe da zai gudana a ranar Aasabar mai zuwa.

Kwamishinan ya bayyana cewa bayan kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya, Sufeto-Janar Alkali Usman Baba ya tara su a matsayinsu na shugabannin rundunar inda ya shaida musu nasarori da akasin haka da aka samu yayin zaɓen da ya gabata.

Tare kuma da nuna musu buƙatar da ke akwai kowa ya ɗora daramarsa tamau domin hana aukuwar saɓanin yayin zaɓe na gaba.

Ya yi amfani da wannan dama wajen tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewar zaɓe mai zuwa zai gudana cikin kwanciyar hankali a jihar, don haka ya kowa ya fito ya zaɓi ra’ayonsa idan lokacin ya zo.

A cewarsa, “Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya tana mai sanar da jama’a da sauran masu sa-ido na ciki da wajen ƙasar nan cewa, da su da sauran jami’an tsaro za su taimaka wa Hukumar Zaɓe gudanar da zaɓen nan cikin lumana.

“Ina kara bayyana ma jama’a da babbar murya babu gudu babu ja da baya cewa duk wanda yake da niyyar satar akwatin zaɓe, ko sayan ƙuri’a, ko d’ɗaukar makami to jami’an tsaro ba za su saurara masa ba.”

“Don mutumin da yake da niyyar ya yi ma wani ko wasu iyayen gida a siyasa, walau ɗaukar mataki ko tada zaune tsaye to ya nesanta kansa daga batun idan ba haka ba kuwa zai fuskanci mumunan hukunci.”

Daga bisani ya buƙaci haɗin kan al’ummar don bai wa ‘yan sanda a jihar damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.