Za mu yi aiki ba dare ba rana don ganin an yi zaɓen gwamnoni lafiya – Hukumomin tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumomin tsaro a Nijeriya, sun bada tabbacin cewa za su yi aiki ba dare ba rana don ganin an yi zaɓukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi lafiya a ƙasar.

Babban mashawarcin tsaro na ƙasar, Janar Babagana Monguno, mai ritaya ne ya bayyana haka lokacin wani taron kwamitin tuntuɓa tsakanin hukumomin tsaro kan sha’anin zaɓe a ƙasar.

Janar Babagana Monguno, ya ce zaɓen gwamnoni da na ‘yan majlisun jihohi na da sarƙaƙiya.

Ya ce, “Zaɓukan gwamnonin sun sha bamban da na shugaban ƙasa don kuwa zaɓe ne guda 1,02, abin da ke nufin za a samu ƙarin mutanen da za fita don kaɗa ƙuri’a.”

Babban mashawarcin tsaron ya ce za kuma a samu ƙarin cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

A don haka, Janar Babagana Monguno, ya ce yana magana da babban hafsan tsaro da kuma babban Sufetan ‘yan sanda na Nijeriya waɗanda ke jagorantar tsare-tsaren zaɓen gwamnonin da ke tafe.

Babban mashawarcin ya ce, dole ne jami’an tsaro su yi aiki bisa doka sannan su bar duk wanda ya cancanta ya kaɗa ƙuri’arsa.

Janar Babagana Monguno, ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa su gargaɗi magoya bayansu a kan su guji tada hankula a lokacin zaɓukan gwamnonin da ke tafe.

A ɓangare guda kuma, rundunar ‘yan sandan Nijeriyar ma ta ce, ta tura ƙarin ma’aikata da kayan aiki don ƙarfafa matakan tsaro lokacin zaɓen gwamnoni mai zuwa.

Rundunar ta kuma ce a baya-bayan nan, jami’anta sun ƙwato miyagun makamai 182 daga hannun mutanen da ake zargi sun mallake su ba bisa ƙa’ida ba.