Daga AISHA ASAS
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗora alhakin faruwar wasu rikice-rikice a sassan ƙasar nan kan attajirai da masu matsayi, tare da shan alwashin yin maganinsu.
Buhari ya yi wannan magana ne a ranar Talata a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar dattawan Barno da Yobe a fadarsa da ke Abuja kamar dai yadda mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya bayyana.
A sanarwar da Femi ya fitar Buhari ya ce, “Muna da buƙatar wannan ƙasa, za mu ci gaba da aiki domin samun daidaito.
“Ina da yaƙinin cewa za mu shawo kan ‘yan tsirarun masu kuɗi da masu matsayin da suke haifar wa ƙasar nan cikas. Da yardar Allah, za mu gano su mu kuma yi maganinsu.”
Shugaban ya ce, “Yana jin cewa duk abin da ya faru hakan ba zai hana cigaba ba, za mu ci gaba da miƙa addu’o’inmu ga Allah domin samun galaba a kan waɗanda ke ganin ba su da buƙatar Nijeriya.”
Game da tarin buƙatun da dattawan suka gabatar don neman a biya musu, Buhari ya ce suna sane da taɓarɓarewar ababen more rayuwa a yankunan, amma cewa a halin yanzu ilimi shi ne fannin da gwamnatinsa ta fi maida hankali don tabbatar da dukkan yaran da suka kai shekarun tafiya makaranta sun samu ilimi in ba haka ba gaba ba zai daɗi ba.