Za mu yi maganin ‘yan fashi da masu tada ƙayar-baya, cewar Buhari

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yayi gargaɗin cewa babu wani sassauci game da matakan da gwamnati ta shirya ɗauka na neman kawar da matsalolin ‘yan fashi da masu tada ƙayar-baya da sauran manyan laifuka da suka addabi al’umma a faɗin ƙasa.

Buhari ya yi wannan gargaɗi ne ta bakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, yayin wani taro kan sha’anin tsaro wanda gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya suka gudanar a Jihar Kaduna.

Buhari ya yarda cewa lallai Nijeriya na fama da matsalolin tsaro, amma cewa ya buƙaci sabbin shugabannin tsaro da samar da sabbin dabaru kuma ingantattu da za a yi amfani da su wajen magance matsalolin.

Yayin taron, Gwamnin Arewa sun yarda za su yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya da ma takwarorinsu na kudancin ƙasa wajen ganin an daƙile matsalolin tsaron.

Taron wanda ya gudana a ranar Alhamis, an yi shi ne a Fadar Gwamnatin Kaduna inda aka tattauna batutuwan da suka shafi fannin tsaron Arewa.

Mahalarta taron su ne, Gwamnan Kebbi da na Jigawa da na Sokoto da Kaduna da Nasarawa da Kano da Katsina da Filato. Sai kuma mataimakan gwamnonin Bauchi da Kogi da Zamfara da Binuwai da kuma Neja.