Za mu yi wa tsaron kasar nan garanbawul – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya ce,  cikin shekara nan mai zuwa zai dau matakan da zai yiwa tsarin tsaron kasar garanbawul. Shugaban ya yi wannan furuci ne, a ya yin da yake nuna farin cikin sa da karbo daliban sakandire ta Kankara da jami’an tsaro su ka yi, a ranar Alhamis ta wannan mako.

Shugaban ya ce, zai yi iya kokarin sa, yaga ya baiwa mara da kunya a harkar tsaro, musamman a yankunan da abin ya ke kara ta’azzara.

“Hakkin mu ne mu samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin jama’a. Koda yake akwai alamun mun gaza, amma za mu cigaba da kokartawa”

“Ina sane da ni na nemi in shugabanci kasar nan, kuma na amince da gazawa ta, amma zan yi iya kokari na in kawo gyara, kuma zan cigaba da yi wa kasar nan biyayya” Inji shugaba Buhari.

Ya kara da cewa ” A kan batun tsaro, shekara mai zuwa za ta zo da sauyi, wadanda su ka rage a matsayin jagororin rundunonin mu na tsaro daga shekara mai zuwa, lallai dole su zage dantse”

Shugaba Buhari ya kara nanata aniyar gwabnatin sa na baiwa jami’an tsaro duk wani tallafi da su ke bukata, wurin ganin sun shawo kan matsalar tsaro a kasar nan.

A karon farko, shugaban ya fito fili ya bayyana wa duniya cewa, jami’an tsaron na Nijeriya sun gaza a ayyukan na su, kuma lallai zai tabbatar sun tashi tsaye akan nauyin da aka daura mu su.

“Jami’an tsaro sun san nauyin da aka daura musu, kuma na kan zauna da su lokaci lokaci akan matsalar tsaro, amma a gaskiya basa aikin su yadda ya kamata” a cewar shugaba Buhari.

Daga karshe ya kara da cewa “Hakki ne a kan mu mu tsare kasar nan, koda yake mun gaza, amma zamu cigaba da kokartawa”.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*