Zafi ya hana mahajjata jifan shaiɗan

Ministan hajji da umarah na ƙasar Saudiyya Dr Abdulfatah bn Sulaiman ya bada umarnin hana mahajjata jifan shaidan daga karfe 11am zuwa 4pm.

Sanarwar tace “an ɗauki matakin hana jifan shaidan daga 11am zuwa 4pm. Akwai jami’an tsaro da zasu tabbatar cewa alhazai sun bu wannan umarni domin rashin bin wannan umarni zai zo da hukunci ” Muna addu’a Allah ya kiyaye mana mahajjata ya kuma amshi ibadunsu.

A wata sanarwar Saudi Gazette, a bana an samu mahajjata kimanin 1,833,164 wanda suka zo daga sassa daban daban na duniya domin sauke farali.