“Tun ina makarantar firamare na fi sauran ɗalibai iya karatun litattafan Hausa”
Daga UMAR GARBA a Katsina
Maryam Nuhu Turau kallabi ce tsakanin rawuna duba da cewa ta yi fice a zahiri da kuma kafafen sada zumunta na zamani, saboda kasancewarta marubuciya, ‘yar kasuwa kuma mai bai wa matasa shawara akan su nemi na kansu. Ta kuma kasance uwa wadda ta kafa ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin marubuta a arewacin ƙasar nan. Wakilin Blueprint Manhaja a Katsina, Umar Garba ya tattauna da Maryam Nuhu Turau a kan batutuwan da suka shafi harkar rubutu, kasuwanci, shawara ga matasa, ƙalubalen da ta fuskanta kafin ta taka matakin da take akai yanzu da kuma nasarorin da ta samu a rayuwa.
MANHAJA: Za mu so jin taƙaitaccen tarihinki?
MARYAM: An haife ni a unguwar Rafin Daɗi da ke nan cikin garin Katsina, na yi makarantar firamare a Rafin daɗi primary school daga nan sai na shiga makarantar sakandare ta ‘yan mata wato WTC inda na yi ƙaramar sakandare, na yi karatun babbar sakandare a Unity Girls Secondary School da ke Jibiya.
Bayan na kammala karatun sakandare a shekarar 2002 na samu shiga makarantar horon malamai wato Federal College of Education da ke nan Katsina a shekarar 2002, bayan na gama karatun NCE a shekarar 2006 na kuma shiga wata makarantar inda na yi Difloma akan ilimin komfuta, na kuma yi karatun addini a Islamiyu daban daban ta yamma da dare don samun ilimin addini haka dai har zuwa lokacin da na yi aure.
Mene ne alaƙarki da marubuta, ko ke ma marubuciya ce?
Eh, ni marubuciya ce sosai ma kuma ina da alaƙa da su shiyasa ake gani na da marubuta, bayan nan ni ma ina da ƙungiyar marubuta don kuwa nice na kafa ƙungiyar marubuta ta Jihar Katsina, inda yanzu haka ni ce mataimakiyar sakatare na ƙungiyar kuma ina cikin ƙungiyoyin marubuta a jihohin Arewa irinsu Kano kuma ina cikin ƙungiyar mawaƙan Najeriya da dai sauran ƙungiyoyin da suka danganci adabi.
Me ya baki sha’awar shiga harkar rubutu?
To, abinda ya ba ni sha’awa har na shiga harkar rubutun litattafai shine tun ina makarantar firamare skul na kasance wadda ta fi sauran ɗalibai iya karatun litattafan Hausa, saboda idan mallam ya shigo aji ana son ayi karatun littafi ni ake kira don na karanta sauran ɗalibai na saurare to, tun daga wannan lokacin na fara jin ina son na fara ƙirƙirar labari da kuma rubutu shi a matsayin littafi.
Idan mai karatu na son zama marubuci ta ina zai fara?
Idan kana son zama marubuci hanyace mai sauƙi musamman idan mutum na da sha’awar farawa, saboda dukkan abinda kake da sha’awa akai bazai wahalar da kai ba. Za ka iya fara tuntuɓar wani ko wata wanda kasan gogagge ne a fagen iya rubutu ƙila kana son ka ɗauki wani batu don kai rubutu a kan shi misali idan kana son yin rubutu kan abinda ya shafi ta’addanci ko shaye-shaye ko kuma shugabanci ko siyasa abinda ya kamata ka yi shine sai ka nemi masana a ɓangaren don su baka shawara game da me ke haddasa al’umma shiga sha’anin ta’addaci ko kuma me ya sa matasa ke shaye-shaye ko kuma ta ya ake fara siyasa irin wannan binciken ya kamata ka yi daga wurin masana sannan kada ka sauka daga kan batun da kake rubutun akai bayan ka kammala rubutun sai kuma ka bai wa masana su duba maka idan akwai gyara a gyara ta haka za ka iya farawa.
A cikin rubuce rubucen da kika yi wane littafi ko labari ya fi shahara a tsakanin al’umma?
Littafin da yafi yin fice shine ‘Duniya ta yi Zafi’ ya yi suna sosai a tsakanin masu sha’awar karatun littattafai kuma shine littafi na na farko dana fara rubutawa duk da a lokacin ban ƙware ba, ban bi ƙa’idojin rubutu ba saboda kasan komai zaka fara daga farko akan samu ‘yan kurakurai amma duk da haka na samu yabo daga wajen mutane wasu ma har kira na suka riƙa yi suna yaba mini hakan ya matuƙar ƙarfafa min gwiwa. Yanzu haka akwai wani littafin da nake rubutawa wanda In sha Allah shima zai ƙayatar ina rubutun ne a hankali saboda binciken da nake yi kafin sakin shi.
Shin kin taɓa shiga gasar marubuta da wasu ƙungiyoyi ko kafafen yaɗa labarai ke shiryawa?
Sosai ma kuwa, na shiga irin waɗannan gasa da ake yi, na taɓa shiga wata gasar marubuta da aka shirya a nan Jihar Katsina, ni ce na zo ta farko cikin marubutan da aka gayyata a lokacin, Kuma kusan duk shekara nikan shiga gasar Hikayata da BBC ke shiryawa marubuta mata, duk da ban taɓa samun nasarar zuwa ta farko ko ta biyu ba amma akwai labarina da ya taɓa zuwa na huɗu, kuma an sha zaɓar labarina cikin labarai 15 waɗanda daga cikinsu ne ake zaɓar na ɗaya da na biyu da kuma na uku, wanda ina sa ran in sha Allan wata rana zan kasance ta farko ɗin.
Shin banda harkar rubutu ko akwai wata sana’a da kike yi?
Ni ai ban son zaman banza saboda haka ina yin sana’o’i, babbar sana’a ta ita ce noma ina noma da damina idan kuma rani ya zo nikan yi noman rani irinsu albasa, tumatir, attarugu da dai sauransu to amma yanzu na ɗan daina noman saboda matsalar tsaro, ina da gona a yankin Batsari to amma tun da aka fara wannan ‘banditry’ ɗin na daina samun damar zuwa gonar saboda a gonakinmu ne ‘bandits’ ɗin suka kafa sansani.
Ina yin kiwo da kuma sayar da turaruka, humra, gyran jiki na amarya da dai sauran sana’o’i da mata ke yi cikin gida.
Wane mataki kike da burin kaiwa a harkar rubutu ko kasuwanci da kike yi?
To, ina da burin kai wa matakin da kowa zai sanni a fagen rubutu ina son na rubutu littafi wanda jami’o’i za su riƙa yin nazari ko amfani da shi wajen koyarwa, duk da cewa yanzu haka ma wasu sun sanni sosai musamman a shafukan soshiyal midiya saboda suna ganin aikace aikace na wasu ma na son yin abota da kai ko ganinka.Ta fannin kasuwanci kuma ina son zama babbar ‘yar kasuwa duk da na yi karatu amma ban mayar da hankali neman aiki ba saboda na fi son kafa kasuwanci na.
Wacce shawara za ki bai wa matasa akan su dage su nemi na kansu?
Gaskiya babu abinda ke ban haushi kamar inga marar sana’a musamman namiji, irin zaman majalisar nan da suke yi ba sana’a, ina ba su shawara akan su dage su kama sana’a, akwai rayuwa ta gaba da zaka yi ko aure idan baka da sana’a ta ya zaka yi auren har ka iya riƙe iyali. Sannan suma mata lokaci ya yi da za su san sana’a bata maza ba ce kawai, a matsayinki na mace za ki iya yin ɗan kasuwanci ko sana’a cikin gida wanda za ki iya taimakon kanki har ma da mai gida akwai sana’o’i na cikin gida da mace zata iya yi kamar ƙunshi, kitso, kayan miya ko sayar da gawayi da dai sauransu.
A lokacin da ba ki aikin komai wane abu ne kike yi don nishaɗantar da kanki?
To a lokacin da ban aikin komai nikan ɗauko littafi ko jarida na karanta saboda a koda yaushe ban gajiya da karatu, wani lokacin kuma ina yin karatun Al’ƙur’ani,wani zubin kuma nikan kunna talabijin ko in shiga soshiyal midiya ina ‘replying’ saƙonni wani lokacin kuma sai in zauna ni da yara mu yi ta raha.
Wane ƙalubale ki ke fuskanta a rayuwa ko kuma a ayyukanki na yau da kullum?
Akwai ƙalubale kam a sha’anin rayuwa, amma ta fanni rubutu babu wani ƙalubale sosai saboda matuƙar kasan aikinka to ƙalubalen baida yawa sosai idan kuma akwai ƙalubale bai wuce zuwan soshiyal midiya ba wanda ya dakusar da harkar rubutu duba da cewa yanzu wasu masu karatu sun fi son karatu a soshiyal midiya duk da cewa wasu rubuce rubucen babu bincike kafin ayi su, sannan akwai rubuce rubucen batsa da ake yi a ɗora a soshiyal midiya wanda ya saɓawa al’ada da addini kuma mu iyaye ne baza mu so yaranmu su ɗauki waya ba suna shiga irin waɗannan shafuka. Ta fannin kasuwanci ko sana’a kuwa shine yanzu nake gaya maka an hana mu zuwa gonakinmu don mu yi noma wanda wannan babban ƙalubale ne, sai kuma mutanen da ke karɓar kaya bashi kuma su hana ka kuɗinka daga ƙarshe wasu sai dai ka bar su da Allah don kuwa ba biya za su yi ba.
Waɗanne nasarori kika samu kawo yanzu?
Alhamdulillah ! an samu nasarori karatun da na yi ina riƙe da satifiket ɗina a yanzu haka nasara ce, sannan na iya sarrafa komfuta don gudanar da ayyuka na shima nasara ce, sannan akwai arziƙin jama’a wasu sun sanka a zahiri wasu online wasu har so suke su yi abota da kai saboda suna jin sunanka. Ta fannin sana’a kuma da nake yi akwai nasarori saboda bazan nema ba in rasa duk abinda kake so za ka yi wa kanka ko yaranka har ma ka yi wa wani.
Hajiya mun gode da samun damar tattaunawa da Blueprint Manhaja.
Ni ma na gode da wannnan tattaunawa, Allah saka da alheri.