
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Dauda Lawal Dare na Jihar Zamfara, ya nanata cewa Gwamnatinsa ba ta neman yin sulhu da ƴan bindiga jihar.
A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya yi hira da BBC Hausa inda aka samu wasu gidajen jaridu sun kuskure fahimta game da abinda ya faɗa a yayin hirar, wanda hakan ya kai ga ruɗar da al’umma.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta yi nasara a faɗanta da ta’addanci ta salo daban-daban wanda hakan ya taimaka wajen fatattakar ƴan bindiga a duk inda suke a jihar.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya yi alƙawari tun gabannin zaɓen 2023 cewa matsalar tsaro ita ce babbar abinda zai fi mayar da hankali a kai idan ya hau mulki, wanda kuma a yanzu ana samun nasara a ƙoƙarinsa na cika alƙawarin da ya ɗauka.
Ya kuma ce tun a karon farko gwamnatinsu ba ta amince da yin sulhu da ƴan bindigar da suka addabi jihar ba, kamar ya yadda ya sha faɗa a hira da manema labarai.
A yayin hirarsa da BBC Hausa, gwamnan ya ce sulhu zai yiwu ne kaɗai a lokacin da ƴan bindigar suka miƙa wuya kuma suka tuba ba tare da wani sharaɗi ba.
Har’ilayau, Lawal Dare ya ce salon da suke bi wajen magance ayyukan ƴan bindiga yana bada kyawawan sakamako, saboda wurare da dama sun fara samun zaman lafiya a sanadiyyar nasarorin kashe da dama daga cikin ƴan ta’addar da kwamandojinsu da dakarun tsaro suke yi.