Zamanintar da sha’anin gona da ƙauyuka ya dogaro da halin da ake ciki da muradun jama’a

Daga MINA

Abokai, yawan gonakin Sin da ake iya shuka amfanin gona kaso 9% kawai na dukkan gonakin duniya, amma Sin ta ciyar da dukkan al’ummar Sinawa da yawansu ya kai kashi 20% na al’ummar duniya da waɗannan gonaki.

Alƙaluman na nuna cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, ƙasar Sin za ta iya samar da kashi 88% na yawan hatsin da al’ummar Sinawa ke buƙata da kanta.

Ba ma kawai Sin ta warware batun samar da isashen hatsi ga al’ummarta dogaro da ƙarfin kanta ba, har ma ta gudanar da nagartattun tsare-tsaren kawar da talauci bisa halin da take ciki, ya zuwa ƙarshen shekarar 2020, an kawar da talauci a duk faɗin ƙasar, kafin shekaru 10 da MƊD ta tsara.

Gudunmawar kashi 70% da ƙasar Sin ta bayar a ɓangaren kawar da talauci, ya sa Sin ta tabbatar da wadatar al’ummar Sinawa, matakin da ya sanya ta shiga sabuwar hanyar zamanintar da sha’anin gona da raya ƙauyuka.

Yau “Duniya a zanen MINA” zai gabatar muku yadda Sin ta gabatar da wannan buri.

Ƙasar Sin ta samarwa jama’arta isashen hatsi da kawar da talauci da tabbatar da zaman wadatar al’ummarta da bunƙasa ƙauyukan duk bisa halin da ake ciki da ma fito da tsare-tsare masu hangen nesa.

A ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Sin, an fitar da wata sabuwar hanya dogaro da kanta ta zamanintar da sha’anin gona da raya ƙauyuka da wadatar da manoma bisa halin da ake ciki da buƙatun al’umma.

Ko shakka babu, wannan sabuwar hanyar da Sin take bi, zai ba da gudunmawa da wayin kai irin na ƙasar Sin wajen daidaita matsalar ƙarancin abinci da gaggauta bunƙasuwar sha’anin gona a duniya, har ma zai ƙara wa duniya musamman ma ƙasashe masu tasowa kwarin gwiwa wajen samun bunƙasuwa mai kyau.

Mai zane, kana marubuciya: MINA