Zamfara: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da shirin rabon tallafin kayan masarufi ga mabuƙata

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da shirin raba tallafin kayayyakin masarufi ga mabuƙata a jihar.

Mai magana da yawun Gwamna, Bala Sulaiman ya ce, bikin ƙaddamarwar ya gudana ne ranar Litinin a ofishin Kwamishinar Jinƙai da ke Gusau, babbn birnin jihar.

Sanarwar da Sulaimanya rattaɓa wa hannu ta ce, Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta miƙa wa Gwamnatin Jihar kayayyakin masurufi da dama don raba wa marasa galihu a jihar.

A cewar sanarwar, Daraktan NEMA na shiyyar Arewa maso-Yamma, Dr. Ishaya Chonoko, shi ne ya wakilci Shugabar NEMA ta ƙasa, Hajiya Zubaida Umar, a wajen bikin

Sa’ilin da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, tallafin ya zo a daidai lokacin da jama’a ke fuskantar ƙalubale daban-daban, wanda hakan zai taimaka wajen rage musu raɗaɗin rayuwa.

“Ina miƙa godiyata ga Shugaban Ƙasa bisa ƙoƙarin da yake wajen daƙile rashin tsaro, wanda ba domin wannan ƙoƙarin nasa ba da babu wata cigaba da za a samu a fannoni rayuwa.

“Ko tantama babu wannan tallafi zai taimaka wajen kwaranye wa waɗanda suka ci gajiyar shirin ƙuncin rayuwa,” in ji Lawal.