Zamfara: Majalisa ta buƙaci Matawalle ya ɗauki mataki kan kuɗaɗen fansho

Daga UMAR M. GOMBE

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnan jihar Bello Matawalle, da ya yi amfani da kuɗaɗen fansho Naira miliyan 500 da ke ɓoye a banki an rasa mai su wajen biyan ma’aikatan gwamnatin jihar da suka yi murabus haƙƙoƙinsu.

Kazalika, majalisar ta buƙaci Gwamnan da ya nemi ganawa da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, da kuma Babban Daraktan Hukumar Fansho ta Ƙasa domin tattauna yadda za a yi a biya ma’aikatan gwamnati a jihar abin da suka tara a can baya.

A cewar Majalisar, “Wannan na daga cikin matsayar da ta cim ma a zaman da ta yi ƙarƙashin jagorancin shugabanta Hon Nasiru Mu’azu Magarya, bayan da ta karɓi rahoton kwamiti na musamman da ta kafa a ƙarshen shekarar da ta gabata don binciken ayyukan hukumomin fansho a jihar.”

Shugaban kwamitin, Hon Nasiru Bello Lawal Bungudu ne ya karanta rahoton kwamitin wanda ya bada shawarwari kan matakin da ya kamata a ɗauka dangane da abubuwan da binciken ya gano.

Daga bisani, ‘yan majalisar sun tofa albarkacin bakunansu kan rahoton binciken inda a ƙarshe suka amince da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Da wannan, ana sa ran Majalisar Zartarwa ta Jihar ta ɗauki matakin karɓo waɗannan kuɗaɗen fansho da ke ɓoye a bankuna a wurare daban-daban domin amfanin ma’aikatan gwamnatin jihar da suka yi ritaya daga aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *