Zamfara: Sanata Marafa ya musanta sauya sheƙa zuwa SDP daga APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattawa ta ƙasa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa na cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar sa ta APC ya koma Social Democratic Party SDP.

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar APC ta ɓangaren Sanata Kabiru Garba Marafa a Jihar Zamfara, Alh. Surajo Maikatako ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Gusau yau Laraba.

Maikatako ya bayyana jita-jitar da akewa Sanata Kabiru Garba Marafa na shirin sauya sheka zuwa SDP a matsayin sharri, mara tushe kuma mara makama.

“Sanata Kabiru Garba Marafa yana nan a APC kuma zai ci gaba da kasancewa a APC duk da irin barazanar da ake yi masa har sai ya yaƙi rashin adalci da rashin haɗin kai a Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara.”

A cewar sa, Sanata Kabiru Garba Marafa bai taɓa tunanin shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa a Jihar Zamfara ba.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa tsohon Sanata Kabiru Garba Marafa ya kasance kodinetan yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na jmJihar Zamfara Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.

Dangane da watan Ramadan, Maikatako ya ce karimcin Sanata Kabiru Garba Marafa a watan Ramadan ya tallafawa da magoya bayan sa sama da mutum 20,000 a jihar.

Maikatako ya buƙaci magoya bayan sanata Kabiru Garba Marafa a Jihar Zamfara da su kwantar da hankulansu da bin doka da oda tare da yin watsi da duk wani yunƙuri da zai kawo rashin zaman lafiya a jihar.