Daga BELLO A. BABAJI
Jihar Zamfara ta zama wacce ke kan gaba a Nijeriya wajen tara haraji a bisa nazarin ‘State’s performance’, bayan fitar da wani rahoton harajin jihohi da aka yi wa laƙabi da BudgIT’s State of States Report 2024.
Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa hauhawar da ɓangaren tara harajin jihar ya yi da kaso 240.44 ya faru ne sakamakon ƙin dogara da Kwamitin Kasafin Asusu na Ƙasa (FAAC) kaɗai da jihar ta yi.
Rahoton, cikin nazarinsa na shekara, ya duba aikin harajin baki ɗaya jihohi 36 na Nijeriya, inda Zamfara daga mataki na 36 a 2023 sai da ta dawo zuwa na 26 a 2024.
Kakakin ya ƙara da cewa, abun da jihar ke samu daga harajin wasu ababe ya ƙaru da kaso 519.71 wanda daga Naira miliyan 412.03 a 2022 sai da ya kai zuwa biliyan N2.55 a 2023.
Bugu da kari, jihar ta tara waɗansu kuɗaɗe daga hayar gidajen gwamnati, hayar filaye, ɓangaren zuba hannun-jari da makamantansu.
Jimillar kuɗin harajin jihar ya ƙaru da kaso 65.35 zuwa N144.95bn a 2023 daga N87.68bn a 2022.