



Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, ya bayyana aniyar gwamantinsa ta ƙaddamar da dokar shirin bada kariya a jihar.
A ranar Laraba ne gwamnan ya karɓi baƙoncin tawagar wakilan Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, (UNICEF) a Fadar gwamnatin jihar.
A wata sanarwa da Kakakinsa Sulaiman Bala Idris ya fitar, wakilin UNICEF a Nijeriya, Cristian Munduate ya bayyana gamsuwarsa ga yadda jihar ta samu ci-gaba a ɓangaren bunƙasa harkokin kiwon lafiya.
Sanarwar ta ƙara da cewa UNICEF, GAVI, WHO da wakilan ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) sun halarci zaman tattaunawa game da batun sanya dokar a jihar.
A lokacin da ya ke magana, Gwamna Dauda ya bayyana Tsarin Jinsi a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin magance matsalolin da ke hana al’umma amfani da damammaki.
Ya ce samar da dokar bada kariya za ta taimaka wajen aiwatar da muradun al’umma musamman marasa galihu.
Ya kuma ce tsarin ƙaddamar da shirin bada kariya ga ƙananan yara don kula da ƴancinsu na ɗaya daga cikin manufofinsu.
Haka kuma ya yi tsokaci game da dokar nakasassu inda ya ce suna ƙoƙarin tabbatar da kula da ƴancinsu da ƙaurace wa nuna musu wariya gami da damawa da su acikin harkokin al’umma.
Akan haka ne gwamnan ya ce za a yi nazari daki-daki tare da samar da kwamiti da zai tabbatar da amsa buƙatun nakasassu da marasa galihu.
Kazalika ya koka ga halin da suka samu ɓangaren kiwon lafiya da kuma nasarorin da suka samu a rabin farko na wa’adin mulkinsa, waɗanda suka haɗa da gyare-gyaren asibitoci da makarantun kiwon lafiya a wasu daga cikin ƙanan hukumomin jihar.
Daga ƙarshe, gwamnan ya yaba da haɗa hannu da UNICEF ganin yadda ke da tasiri ga ci-gaba a harkar lafiya a jihar.