Zan ƙara ƙoƙarin kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas – Turakin Ƙofa

Manhaja logo

Daga DAUDA USMAN a Legas

Babban Shugaban kulawa da cigaban kasuwancin ɓangaren citta da tafarnuwa a kasuwar Mile12 da ke cikin birnin Jihar Legas, Alhaji Yusif Daud Ƙofa kuma Turakin Ƙofa ta Jihar Kano ya bayyana cewa, zai ƙara ƙoƙari wajen kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas da kewayanta gaba ɗaya.

Turakin Ƙofa ya yi wannan tsokaci ne jim kaɗan bayan kammala taron ƙaddamar da su a matsayin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta mile12 waɗanda za su cigaba da jagorantar ɓangarorin kasuwancin kasuwar ta mile12 a makon da ya gabata.

Shuwagabannin ɓangarorin da kasuwar ta ƙaddamar akwai shi kansa Alhaji Yusuf Dauda Ƙofa a matsayin shugaban ɓangaren citta da ta farnuwa da Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano a matsayin shugaban ɓangaren tumatiri da Alhaji Aminu musa Kiru shugaban ɓangaren tattasai tarugu da shambo da sauran waɗanda lokaci ba zai bari a cigaba da zayyano sunayen suba a wannan lokaci.

Da yake bayyana wa ‘yan jaridar farin cikin sa tare da jin daɗinsa a legas bis aga gaskiyar wannan al’amari bayan kammala taron ƙaddamarwar Turakin na Ƙofa ya cigaba da nuna farin cikin sa tare da jin daɗinsa a game da wannan matsayi da Allah Ubangiji yabashi ’yan kasuwar ɓangaren sa na kasuwancin citta da tafarnuwa suka sanya hannuwan su bibiyu shugaban kasuwar Alhaji Shehu usman jibirin samfam ya tabbatar masa da ita kuma ya ƙaddamar da shi a matsayin shugaban ɓangaren gudanar da harkokin kasuwancin citta da ta farnuwa alegas da kewayanta gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa, zai ƙara ƙoƙari wajen kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas da kewayanta gaba ɗaya.

Hakazalika, ya cigaba da cewa, akan hakan ya ke isar da saƙon godiyarsa ga shugaban kasuwar Alhaji Shehu usman jibirin samfam tare da ’yan vangaren sa na kasuwancin citta da tafarnuwa alegas injishi da manyan iyayan kasuwar ta mile12 ya ce yana godiya kwarai da gaske bisaga wannan karamcin da zukayi masa acewar sa da fatan Allah Ubangiji ya sakamasu da alheri.

Ya ce, iyayan kasuwar ta mile12 sun haɗa da shugaban ƙungiyar dattawan kasuwar Alhaji Isa mohammed mai shinkafa da Alhaji Habu faki garkuwan faki da Alhaji Haruna Mohammed ta Marke mai dankalin Turawa da Alhaji Abdulwahab tsoho Babangida sakataren ƙungiyar Dattawan kasuwar.

Da fatan Allah Ubangiji ya sakamasu da alheri bisaga ƙoƙarin su na haɗa kawunan ’yan kasuwa tare da kawo zaman lafiya akasuwar ta mile12 baki ɗaya sannan kuma ya cigaba da jawo hankulan abokan aikinsa na ofishin sayar da citta da citta da ta farnuwa dasu ƙara ƙoƙari awajan bunƙasa harkokin kasuwancin citta da tafarnuwa akasuwar ta mile12 dama jihar a legas baki ɗaya.

Ya ce abokan aikin nasa sun haɗa da mataimakin sa Alhaji Abdulrahaman da Alhaji Sunusi Abubakar sakataren ƙungiyar ta, yan citta da tafarnuwa gaba daya da sakataren kuɗi Abubakar magaji da ma’ajin ƙungiyar Alhaji Danladi Usman sauran sun haɗa da Alhaji Tasiu Dam Baba Alkalin ƙungiyar da Muktar Ɗan kakan mataimakin sakataren kuɗin ƙungiyar da sauran makamantan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *