Daga DAUDA USMAN
Sabon Shugaban ƙungiyar Direbobin J5 ta ƙasa, ƙarƙashin NURTW reshan Jihar Legas da ke shiyar unguwar mile12 a Legas, Kwamaret Umar Ahmed Isah ya yi alƙawarin cewa zai bayar da ɗimbim gudunmawa wajan kawo cigaban ƙungiyar a jihar da kewayenta gabaɗaya.
Kwamaret Umar Ahmed Isah ya yi wannan tsokacin ne a ofishin ƙungiyar da ke kasuwar mile12 a lokacin da suke karɓar baƙuncin waɗansu daga cikin ‘yan ƙungiyar ta J5 na unguwanni daban-daban a cikin garin Legas da suka zo taya shi murna tare da fatan alheri dangane da samun wannan matsayi.
Sabon shugaban ƙungiyar ta J5 na yankin unguwar mile12 kwamaret Umar Ahmed Isah ya yi jawabin godiya ga shugabannin ƙungiyar tare da nuna farin cikinsa dangane da samun wannan muƙamin.
Ya cigaba da gabatar da jawabin sa na godiya ga shugabannin ƙungiyar da wakilanta na unguwanni daban-daban da ke cikin garin Legas waɗanda suka hango cancantarsa suka ba shi haɗin kai da goyan baya aka ba shi wannan matsayi kuma suka tabbatar masa da shi a nan take.
Ya ce, yana yi wa dukkansu fatan alheri tare da fatan Allah Ubangiji ya sakawa kowa da gidan aljannah.
Ya ƙara da cewa, kuma zai yi iyakar ƙoƙarinsa a wajen kawo cigaban ƙungiyar tare da kare mutuncinta a Legas da gabaɗaya.
Hakazalika, ya cigaba da gabatar da saƙon godiyarsa ga shugaban kasuwar mile12 Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam Dallatun Egaland a Beokuta ta Jihar Ogun, wanda a cewarsa, shi ne ya tsaya tsiyin-daka domin ganin ya samu shugabancin ƙungiyar ta J5 na shiyar mile12 da kewayenta gabaɗaya.
Ya ce, Allah Ubangiji ya yi masa sakamako na alheri. Sannan ya cigaba da jawo hankulan abokan aikinsa na ƙungiyar ta J5 da mambobinta da kuma dukkan masu ruwa da tsaki na ƙungiyar a shiyar unguwar mile12 da su zo su haɗa kawunan junansu su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya domin ciyar da ƙungiyar gaba.