Zan bai wa ƙananan hukumomi ’yancin kansu idan na zama Gwamnan Kano, Cewar Gawuna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alƙawarin bai wa ƙananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Kano.

Gawuna ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wani shiri na gidan talabijin ɗin NTA mai suna “The Balot”.

Ya ce: “Ƙananan hukumomi wani ɓangare ne na gwamnati wanda ya fi kusa da jama’a wanda ke taimakawa wajen cigaban al’umma ta kowacce fuska,” inji Gawuna.

“A matsayina na tsohon shugaban ƙaramar hukumar na san abin da ya shafi gudanar da mulkinta.

“Lokacin da nake shugaban ƙaramar hukuma, an ba ni damar yi aiki na yadda ya kamata, hakan ta sa muka samu nasarori da dama, don haka idan aka zaveni a matsayin Gwamna ni ma zan ba su damar cin gashin kansu,” Gawuna ya jaddada.

Ya ƙara da cewa shi ne wanda ya fi cancanta kuma a shirye ya ke ya zama Gwamnan Jihar Kano bayan ya yi aiki da gwamnatocin da suka gabata kuma ya samu ƙwarewa da dama, duk da haka ya bada tabbacin zai ɗora kan ayyukan da suka samu nasara akai kuma na kaucewa kura-kuran da su kai.

A sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aike wa manema labarai a Kano, Gawuna ya kuma buƙaci al’umma musamman matasa da su guji tada hargitsi yayin zaɓe da bayan zaɓe don inganta zaman lafiyar da ake da shi a Kano.