Daga AMINA YUSUF ALI
A cikin abin da ya kira da aikinsa ba ƙarshe a gadon mulki, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya roƙi ‘yan Nijeriya yafiya idan akwai inda aka samu wani tsari daga tsarukan da gwamnatinsa ta gudanar da ya yi wa wani a cikinsu ciwo a cikin shekaru 8 da ya shafe a kan gadon mulki.
Shugaban kasar ya yi wannan kira ne a wani jawabi da ya yi a wani shiri da ya gabatar kai tsaye a ranar Lahadin da ta gabata.
Buhari zai mika ragamar mulki ga sabuwar gwamnati a ranar Litinin. A cikin jawabinsa na barin gado ya bayyana cewa: “‘Yanuwanan ‘yan Najeriya maza da mata, da abokan Nijeriya”.
“Ina yi muku jawabi a yau, a matsayin aikina na ƙarshe a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na wannan ƙasa tamu mai albarka, cikin godiya mai tarin yawa ga Allah subhanahu wa ta’ala, ina godiya mai tarin yawa ga ‘yan Nijeriya da kuma jin daɗi maras misaltuwa”. Inji shi.
Ya ara da cewa: ” A yau ne muke yin bukin murnar canza hannun mulki daga wata gwamnati zuwa wata cikin lumana, a ƙoƙarinmu na ganin mun inganta kuma mun ɗorar da Dimokuraɗiyyar Nijeriya”.
Daga nan ya ƙara da cewa: A wannan shekarar Nijeriya ta shaida mafi ingancin zaɓen shugaban ƙasa wanda ba a taba yin irinsa ba tun a jamhuriya ta 1. A cewar sa wannan yana nuna cewa, kullum ana ƙara samun cigaba a zaɓuɓɓuka a ƙasar nan.
“Dukkanmu a matsayinmu na al’umma guda dole mu dage mu cigaba da ririta alfanun da muka samu a tsarin gudanar da zaɓen domin bin matakan da ita ma Nijeriya za ta shiga sahun sauran ƙasashe”.
Haka kuma ya ƙara da cewa, Demokraɗiyyar Nijeriya ta ba da dama kuma tana kuma tana ƙarfafa gwiwar waɗanda suke jin an musu rashin adalci, inda ta ba da dama ga wasu ‘yan takara da jam’iyyu da ba su amince da sakamakon zaɓe ba da su je kotu.
“Ina jinjina ga ‘yan takarkarun da suka yi takarar shugabancin ƙasa tare da jam’iyyunsu da suka amince da tsarin shari’armu, har ma suka kai kokensu na zaɓe zuwa kotu”.
Haka ya yi kira a matsayinsa na shugaban ƙasa da ‘yan Najeriya su haɗa kai su dage wajen kawo cigaban alkhairi a ƙasar.
“Ga ɗanuwana kuma, aboki, sannan abokin aiki na gwagwarmayar siyasa na fiye da tsahon shekaru 10 – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu -, Ina taya ka murnar cikar burinka, wanda tsananin shauƙin son sanya Nijeriya cikin manyan ƙasashen duniya ne musabbabinsa”.
“Haƙiƙa ka yi aiki tukuru don ganin wannan rana, kuma Ubangiji ya dubi ƙoƙarin naka. Ina da tabbacin cewa, shauƙinka na yin zarra, zama abin dogaro, a kan daidaito da adalci a dangantaka da dagewa don tabbatar da daidaito, biyayya ga ƙasa da kuma burin Nijeriya ta zama mai muhimmanci a idon duniya dukkansu za ka iya cimma su da ikon Allah, a yayin da kake shugabantar ƙasarmu i zuwa babban mataki, bayan tafiyata”.
“Kai ne mafi cancanta daga kafatanin dukkan ‘yan takara kuma ‘yan Nijeriya ba su yi zaɓen tumun dare ba”.
“Shekaru takwas da suka wuce sun kasance wani juyi ne mai mai cike da azama a burina da jajircewata na ganin Nijeriya ta samu dukkan buƙata”.
“‘Yanuwana ‘yan Nijeriya, a game da ƙwaƙwaran goyon bayan da kuka ba ni da ni da jam’iyyata, na fara wannan tafiya cike da alƙawurra da tsammani daga gare ku. Ba na son a ce ni kaɗai ne mai gyaran siyasa ba, amma ina son na yi abinda ya dace da zai samar da tasiri mai ma’ana a kan rayuwar talakan Nijeriya.
“Wannan tsammani bai tashi a banza ba saboda ni kamar sauran talakawan Nijeriya ina sane da yadda ƙasar take ta ƙara cigaba da taɓarɓarewa ga barin tsarin gaskiya”.
Sannan kuma a cewar sa, ya bar gadon wani tsarin zaɓe wanda tilas zai sa shugabanni su zama masu riƙe amanar talakawa. Wato tsarin da zai tabbatar da cewa ƙuri’ar talaka ta zama mai amfani kuma zaɓen da sakamakon zave su zama sahihai. Sannan a rage yawan amfani da kuɗi wajen maguɗin zaɓe, sannan ‘yan Nijeriya su zaɓi shugabannin da suke da ra’ayi.
Kuma a cewarsa kwalliya ma har ta biya kuɗin sabulu. Domin a zaɓen bana ‘yan siyasa da dama marasa kuɗi, marasa iyayen gida sun kayar da ‘yan takara masu farcen susa.
Haka a cewar sa, gwamnatinsa ta ɗau matakai da dama don ceto tattalin arziki ƙasa a yayin da tattalin arzikin duniya yake cigaba da jin jiki.
Kasancewar a cewar sa, kowa shaida ne a kan yadda tattalin arzikin duniya ya ji jiki a tsakanin 2020 da 2022 sakamakon annobar COVID-19. Har yanzu kuma a cewar sa, matakan da gwanatinsa ta ɗauka na ceto tattalin arzikin har yanzu ba shi da na biyu a faɗin duniya.
Bugu da ƙari a cewar sa, gwamnatinsa ta ƙara faɗaɗa dama ga mazauna karkara a Nijeriya da su samu abin yi da kuma samar da abinci ga miliyoyin ‘yan Nijeriya mazauna ƙauye, da ba wa matanmu dama su samu sana’o’i.
A cewar sa: “Matasa ma maza da mata ma mazauna birane an tallafa musu don amfani da dabarun sana’o’in da suka iya. Gwamnatinmu ta ba wa kamfanoni masu zaman kansu damarmaki don yin kasuwancinsu domin tabbatar da samun ribarsu”.
Hakan a cewar sa, saboda kamfanoni masu zaman kan nasu suna taimakawa matuqa wajen tabbatar da tattalin arziki mai ƙarko.
” A ƙoƙarinmu na farfaɗo da tattalin arziki, mun yanke hukunci masu tsauri, waɗanda kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Wasu matakan kuma sun jawo shan wahala da rashin jin daɗi na wucin gadi, wanda nake mai ba da haƙuri ga ‘yanuwana ‘yan Nijeriya, amma mun ɗauki waɗannan matakai ne saboda saboda gyaruwar ƙasar.
Sannan a cewarsa, gwamnatinasa ta kammala wasu ayyuka masu yawan gaske domin don samun cigaban ƙasa. Kamar, dokar kamfani raba man fetur, wasu ayyuka na samar da wutar lantarki da kammala gadar Neja ta biyu da kuma wasu hanyoyi da suke kan titunan zuwa garuruwa da ƙasashe.
Haka a cewar sa, a ƙoƙarinsa na ganin ‘yan Nijeriya sun zauna cikin lafiya da lumana, a cewar sa: “A yayin da nake kammala wa’adina a kan mulki, mun samu damar rage yawan ta’addanci, fashi da makami da afkuwar sauran laifuffuka”.
Kuma a cewar sa, don cin gajiyar wannan ƙoƙari nasa, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da au zama masu kula kuma su zama masu taimaka wa jami’an tsaro.
Sannan ya ƙara da cewa, har yanzu yana cikin alhinin yaran da suke a hannun masu garkuwa, da kuma waɗanda suka rasa danginsu a hatsaniyar tashin tsaro. Kuma ya ce har yanzu jami’an tsaro suna nan suna aiki ba hutu don ganin an sake su ba tare da sun ƙwaru ba”.
Sannan ya ƙara da cewa, a matsayinsa na mai son ganin cin hanci da rashawa sun bar ƙasar nan, ya yi iya ƙoƙarinsa don daƙile shi. Sannan kuma a cewarsa ya samu nasara sosai a wannan ɓangaren, don ya dawo da kuɗaɗe da dukiyoyi da dama da aka yi almundahanarsu.
Ta fuskar hulɗa da ƙasar waje kuwa, Nijeriya tana cigaba da samun tasiri a idon duniya.
Haka ya yi godiya da yabawa ga mambobin majalisar dokokin Nijeriya, saboda biyayya ga ƙasa da riƙe aikinsu.
Daga ƙarshe-ƙarshe, ya gode wa ‘yan Nijeriya waɗanda suka ba da gudunmowarsu da ƙwarin gwiwa don yin wannan namijin aiki na ciyar da ƙasar gaba..
“Ba zan iya mantawa da miliyoyin mutanen da suka yi min addu’a ba a yayin da na yi rashin lafiya a zangon farkon mulkina. Ni ma kullum ina muku addu’a da ma Nijeriya don ta samu ci gaba”. Inji shi.
A qarshe kuma ya ce: “A yanzu da zan koma gidana na Daura, jihar Katsina, ina cike da gamsuwar cewa, na sanya harsashin sake sabuwar Nijeriya ta hanyar fara ɗaukar matakai na farko kuma ina da yaƙinin wannan sabuwar gwamnatin da za ta hanzarta wajen tabbatar da wannan tafiya don ganin Nijeriya ta cika burinta na zama ƙasa gagara gasa,” a cewar sa.
“Ina da yaƙinin cewa zan bar mulkin Nijeriya a 2023 fiye da yadda na same ta a 2015.
“Ina godiya ga kowa, kuma Allah ya albarkaci Jamhuriyar dimokuraɗiyyar Nijeriya”.