Zan ci gaba da raba tallafi har zuwa ƙarshen mulki na, inji Zulum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da rabon tallafin kayan abinci ga marasa galihu da kuma al’ummomin da tashin hankali ya shafa iya tsawon mulkinsa.

Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin da ya ke ƙaddamar da rabon kayan tallafin na Gwamnatin Tarayya ga gidajen dubu 100,000.

Zulum ya ce yayin da Gwamnatin Tarayya ta samar da gidaje 100,000, gwamnatinsa na samar da ƙarin gidaje 300,000 don su zama gidaje 400,000.

Ya bayyana cewa lamarin Borno ya sha bamban saboda wasu yankunan da ‘yan tada ƙayar baya suka ɓarnata kuma har yanzu waɗanda suka dawo ba su samu cikakkiyar damar shiga gonakinsu ba, don haka akwai buƙatar a ci gaba da tallafa musu.

“A yau mun zo ne domin ƙaddamar da rabon kayan agaji ga marasa galihu 100,000 a Borno ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa baya ga gidaje 300,000 da za su ci gajiyar tallafin na jihar,” inji Zulum.