Zan haɗa kan ‘yan Nijeriya idan na lashe zaɓe – Atiku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya samu gagarumar tarba cikin ƙasaitaccen biki a garin Jada, wanda nan ne mahaifarsa.

Da ya ke masa maraba, cikin ƙasaitaccen yanayi da aka shirya na musamman, shugaban ƙaramar hukumar Jada Honorable Salisu Muhammed Solo ya ce, suna mutuƙar alfahari da kasancewar Atiku ɗansu, inda ya yi alƙawarin mara masa baya a takarar shugabancin Nijeriya da ya ke yi. 

A jawabinsa yayin taron, Sanata Dino Melaye ya bayyana muhimmancin ziyayar zuwa gida, inda yace wannan ya nuna cewar Atiku ya san asalin sa ba kamar wasu yan takarar ba waɗanda suke cike da rudani game da asalinsu.

Ya ce, Atiku shi ne ɗan takarar da ya fi cancanta kasancewarsa ba mai ƙabilanci ba wanda ya ke da dukkan abinda ake buƙata domin ceto Nijeriya daga mummunan yanayin da ta ke ciki.

Gwamnan jihar ta Adamawa Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri godewa Atiku ya yi saboda shigowa cikin al’umar sa. Inda ya bawa ɗan takarar ta PDP tabbacin cewar za su yi aiki domin nasarar sa a zaven, domin bashi damar amfani da ƙwarewarsa da kishinsa wajen ceto Nijeriya.

Da ya ke mayar da jawabi, ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya gode wa mutanen nasa saboda addu’o’in su da fatan alheri.

Ya kuma yi kira gare su da su sauke nauyin dake kan su na yin zaɓe domin ba shi damar karvar ƙasar don inganta makomar kowa, inda ya jaddada aniyarsa ta kasancewa jakada na gari ga mutanen sa da ƙasar baki ɗaya inda ya yi alƙawarin aiki domin dawo da zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban ƙasa idan aka zaɓe shi.

Hakan na ƙunshe ne a bayanin da Mataimaki na Musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai, Abdulrasheed Shehu ya fitar.