Zan kafa gwamnatin nagarta da dacewa ba ta haɗin kan ƙasa ba – Tinubu

Daga AMINA YUSUF ALI

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da suke a dukkan faɗin jam’iyyu mabanbanta da su ba da goyon baya ga gwamnatin da yake shirin kafawa a Nijeriya, yayin da ya bayyana cewa, ba zai yi kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa ba idan aka rantsar da shi, sai dai ya amince zai tafiyar da gwamnati mai nagarta.

Tinubu ya ƙara da cewa, a yayin da zai zaɓi masu taimaka masa a fadarsa ta shugabancin ƙasa, zai zaɓa ne bisa la’akari da cancanta da dacewa.

Wannan jawabi yana ƙunshe ne a wani saƙo da Tinubun ya aike ga ‘yan Nijeriya wanda ya sanya wa hannu da kansa. Ya bayyana cewa shirinsa shi ne ninka bunƙasar tattalin arzikin ƙasa (GDP), samar da isasshen abinci, inganta masana’antu, da sauransu, inda matasa za su samu isasshiyar damar gina kawunansu kuma su cimma burikansu.

Tinubu ya ƙara da cewa, sannan yana da burin inganta ƙasar ya ciyar da ita gaba shi ne zai zama babban muradinsa. Saboda haka ba zai yiwu a ce an kasa cimma wannan manufa ba saboda alfarmar siyasa. A cewar sa, siyasa ya kamata a jiye ta a can ƙurya don cimma muradun bunƙasar ƙasa.

A cewar sa: “A matsayina na shugabanku mai jiran gado, na ɗauki wannan nauyi da aka ɗora min. Ana ta surutu a kan gwamnatin haɗin kan ƙasa. Ni kuma burina ya fi gaban haka, ni gwamnatin dacewa nake nema. A yayin zaɓen mataimakan gwamnatina, zan fi duba cancanta da ƙwarewa”. Inji shi.

A cewar sa, zamanin alfarmar siyasa ta wuce. Zai zaɓi ƙwararrun maza da mata ne kawai a faɗin Nijeriya don gina ƙasar, ba tare da la’akari da addinansu ko siyasarsu ba, nagartarka ita za ta sama maka matsayi a gwamnatinsa. Domin a cewar sa gwamnatinsa tana da ayyukan raya ƙasa da dama da take so ta yi bisa inganci.

Da yake tsokaci a kan batun mutanen da suka ƙi zavarsa a zaɓe, Tinubu ya ka da baki ya ce, gwamnatinsa za ta dage wajen kare haƙƙoƙin waɗannna mutanen don a bi musu kadinsu a shari’ance.

Hakazalika kuma a cewar sa, ya shirya tsaf don tafiyar da mulkin da zai taimaka wajen yin ayyukan da za su amfani dukkan mutanen ƙasar waɗanda suka zaɓe shi ko waɗanda ma ba su zaɓe shi ba.

A cewar sa wannan ba lokaci ne na zafafa adawar siyasa ba, don hakan zai iya jawo matsala babba a mulki.

A game da zancen nan mai yamutsa hazo na canjin fasalin Naira da ƙarancin takardun kuɗi, Tinubu ya ce ai wanna zance ya zama tarihi tunda kotun ƙoli ta ba da umarnin a cigaba da amfani da tsofaffin takardun Naira.

Daga ƙarshe ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da waɗanda suka zaɓe shi da waɗanda ba su zaɓe shi ba, da su mara masa baya don ciyar da ƙasar gaba.