Zan taimaki Nijeriya wajen yaƙi da matsalolin tsaro muddin na lashe zaɓe – inji Bazoum

Daga WAKILIN MU

A makon da ya gabata ne ɗan takarar Shugaban Ƙasar Nijar ƙarkashin jam’iyyar PNDS Tarayya, Alhaji Mohammed Bazoum, ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara ta musamman a Daura domin neman goyon bayansa.

Yayin ziyarar, Buhari da Bazoum sun tattauna muhimman batutuwa ciki har da batun takarar Bazoum da batun kwararar ɓatagari daga Nijar zuwa Nijeriya da kuma akasin haka.

Haka nan tattaunawar tasu ta taɓo batun matsalolin tsaron da Nijeriya ke fama da su da zimmar Bazoum zai taimaka wa Buhari wajen yaƙi da matsalolin idan ya lashe zaɓe mai zuwa.

Bazoum bai bar Nijeriya ba sai da ya ziyarci Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da na Jigawa Muhammad Badaru da kuma Sarkin Kano inda bakiɗayansu ya samu tattaunawa da su.

A cewar shugabar magoya bayan Bazoum a Nijeriya, Hajiya Nusaiba Zubairu, Bazoum ya bai wa Buhari tabbacin cewa muddin ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Nijar da za a sake gudanarwa, jami’an tsaron Nijar za su bai wa na Nijeriya cikakken haɗin kai wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suka yi wa Nijeriya tarnaƙi.