Zan yi aiki da kai – Buhari ya taya zaɓaɓɓen gwamnan Anambara murna

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya taya sabon zaɓaɓben gwamnan jihar Anambara, Farfesa Charles Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA, murnar nasarar da ya samu a zaɓen jihar Anambara da ya gudana a ƙarshen makon da ya gabata.

Buhari ya taya Soludo murna ne ta hanyar wallafa saƙon a shafinsa na facebook, tare kuma da yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da zaɓen ya gudana lami lafiya, da kuma hukuma INEC dangane da nasarar gudanar da zaɓen da ta samu duk da irin tulin ƙalubalen da ta fuskanta.

Buhari ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga sabon Gwamnan Anambara, da ya haɗa kai da masu ruwa da tsaki na jihar wajen magance ƙalubalan da Anambara da yankin Kudu-maso-yamma baki ɗaya ke fuskanta.

Haka nan ya ce, “Ina sa ran yin aiki tare da shi don samar da zaman lafiya da tsaro cigaban Anambara da ma ƙasa baki ɗaya.”

Da safiyar Laraba Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Farfesa Chukwuma Soludo na jami’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambara da aka gudanar ran 6 ga Nuwamba.

Bayan ƙidayar ƙuri’u, INEC ta ce ƙuri’u 112,229 Soludo ya samu wanda hakan ya ba shi nasara a kan ɗan takar PDP, Mr Valentine Ozigbo wanda ya samu ƙuri’u 53, 807, wato shi ne dan takara na biyu mai mafi yawan ƙuri’u. Sai kuma ɗan takarar APC, Sanata Andy Uba da ya zo na uku da ƙuri’u 43,285.