Zan yi aiki tuƙuru kafin na koma Daura in ci gaba da kula da dabbobina a 2023 – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce zai mayar da hankali wajen cigaban Nijeriya da al’ummarta kafin ƙarshen wa’adinsa, inda ya ce zai koma mahaifarsa Daura da ke Jihar Katsina domin ci gaba da kulawa da gona da kuma dabbobinsa.

Shugaban ya bayyana haka ne tare da hotunan bikin zagayowar haihuwarsa wanda ofishin jakadancin Nijeriya a ƙarƙashin Ministan Kula da Harkokin Ƙasashen Waje, Mista Geoffery Onyeama suka yi masa ba-zata a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya.

Buhari wanda ya tafi ƙasar Turkiyya domin halartar taro, a ranar Juma’a ya cika shekara 79 da haihuwa.

A cewar mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, Shugaba Buhari ya yanka kek ɗin murnar zagayowar haihuwar tasa wanda ke ɗauke da launin tutar Nijeriya.

Da yake maida jawabinsa a wajen yanka kek ɗin, Shugaba Buhari ya ce zai yi ƙoƙari wajen ciyar da Nijeriya da al’ummarta gaba kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa da zai koma Daura don ci gaba da aikin gona da kula da dabbobinsa.

Buhari a cikin gonarsa

“Ina fatan zuwa 2023 idan na kammala wa’adina na koma gida na kula da gonata. Amma kafin wannan lokacin zan yi iya ƙoƙarina wajen ciyar da ƙasa da al’ummarta gaba da gudanar da ayyuka kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada,” kamar yadda shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya ce ashe bai guje wa bikin haihuwarsa ba a Abuja kuma haka ma a Turkiyya sai da aka haɗa masa bikin.

Ranar Alhamis ce dai Shugaba Buhari ya tafi ƙasar Turkiyya domin halartar wani taro.