Daga DAUDA USMAN a Legas
Sabon shugaban kulawa da cigaban kasuwancin tattasai, atarugu da shambo a Kasuwar Mile 12 dake Legas, Alhaji Aminu Musa, ya bayyana cewar zai yi iyakar ƙoƙarinsa wajen kawo cigaban kasuwancin tattasai, tarugu da shambo a Legas.
Alhaji Aminu Musa ya yi wannan tsokaci ne a ofis ɗin sa dake kasuwar Mile-12 a Legas a lokacin da yake karvar baƙuncin waɗansu daga cikin ‘yan kasuwar waɗanda suka zo taron walimar taya shi murnar zama sabon shugaban ɓangaren tattasai, tarugu da shambo.
Aminu ya ce yana yi wa kowa fatan alheri dangane da wannan al’amari, da fatan Allah Ubangiji ya saka wa kowa da alheri, sannan kuma ya cigaba da nuna rashin jin daɗin sa game da furucin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na janye tallafin man fetur wanda gwamnati Nijeriya take yi domin ‘yan ƙasa su samu sauƙin tsadar rayuwa idan hakan ta tas.
Ya cigaba da cewar idan kuma har gwamnatin Nijeriya ba ta janye wannan furuci ba a cewar sa wannan al’amari ba zai haifar wa ‘yan Nijeriya ɗa mai ido ba wajen gudanar da harkokin rayuwar su ta yau da kullum.
Ya yi wa gwamnatin Nijeriya mai adalci a ƙarƙashin jagorancin adalin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda ake yi masa kyakkyawan zato na alheri zai yi wani abu dangane da wannan al’amarin.
Haka zalika ɗaya daga cikin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta Mile-12, Alhaji Dahiru Rano kuma shugaban ɓangaren sauke kayan boko a kasuwar, inda shi ma ya tofa albarkacin bakinsa dangane da wannan al’amarin inda bayan ya kammala yi wa Alhaji Aminu Musa murnar samun zama sabon shugaban ɓangaren kulawa da cigaban kasuwancin tattasai a Legas sannan kuma ya cigaba da bayyana irin matsalolin da yake ganin janye tallafin man fetur zai haifar wa ‘yan Nijeriya idan hakan ta taso.
Ya ce farko dai ‘yan Nijeriya za su qara samun tsadar rayuwa tunda dukkan kayan abinci da sauran kayayyakin da ake amfani da su domin kyautata wa rayuwa za su yi tashin gwauron zabi da sauran makamantansu, ya ce akan haka yake ganin ya kamata ya bai wa gwamnati shawarar da ta yi wani abu bisa kan wannan al’amari.