Daga DAUDA USMAN a Legas
Sabon shugaban Ƙungiyar Direbobi NURTW, reshen Jihar Legas reshan wanda yake zaune a unguwar mile12 da ke ƙaramar hukumar Ikosi Isheri, Kwamared Ado Yahaiya Barau Kiru ya bayyana cewa, zai yi duk mai yiwuwa wajen kawo cigaban ƙungiyar baki ɗaya.
Kwamared Ado Yahaiya Barau ya bayyana haka ne a ofishin ƙungiyar da ke unguwar mile12 jim kaɗan bayan da shugabannin ƙungiyar ta direbobi da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin ƙungiyar suka ƙaddamar da shi a matsayin sabon shugaban ƙungiyar na reshan unguwar mile12 a Legas.
Ado Yahaiya ya yi jawabin godiya tare da nuna jin daɗi dangane da wannan al’amari inda ya cigaba da shaida wa Jaridar Blueprint Manhaja a Legas cewa, haƙiƙa yana mai nuna farin cikinsa tare da jin daɗi a game da wannan muƙamin da Allah Ubangiji ya ba shi.
Ya ce, ƙungiyar ta direbobi ta tabbatar masa da butin sa a wannan lokaci, ya ce, da fatan Allah ubangiji zai ba shi ikon gudanar da jagorancin al’ummar ƙungiyar a cikin adalci.
Ya ƙara da cewa, kuma zai yi iyakar ƙoƙarin sa a wajen kare mutuncin ƙungiyar da kawo cigabanta gabaɗaya.
Haka zalika, ya cigaba da isar da sakon godiyarsa ga iyayen da shugabanni tare da sauran masu ruwa da tsaki bisa harkokin ƙungiyar.
Ya ce, da fatan Allah Ubangiji ya saka wa kowa da alheri.
Ya kuma isar da saƙon wata godiyarsa ga shugaban kasuwar mile 12 Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam Dallatun Egaland Abeokuta ta jihar Ogun, a cewarsa bisa ga ƙoƙarin da ya yi tare da gudunmawar da ya ba shi a wajen ganin ya samu wannan matsayi.
Ya ce, Allah Ubangiji ya saka masa da alheri, inda ya jawo hankulan mambobin ƙungiyar ta NURTW da ke shiyar mile12 da su zo su haɗa kawunan junan su kuma suhada ƙarfi da ƙarshe domin ciyar da ƙungiyar gaba.
Haka kuma ya cigaba da jawo hankulan direbobinsa na NURTW masu ɗauko fasinja daga Legas zuwa arewacin Nijeriya da su cigaba da yin tuƙi a cikin natsuwa tare da kaucewa shan ƙwayoyi a lokacin da suke tuƙi domin samun sauka lafiya.