Zanga-zanga kaɗai ba za ta kawo gyara a Nijeriya ba – Osinbajo

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya faɗa wa ƴan Nijeriya da sauran sassan Afirka cewa lallai zanga-zanga ba za ta isa magance matsalolin harkokin siyasa ba.

Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙara wa juna sani game da fasaha da harkar jarida ta zamani, shugabanci da sauran su.

Ya ce za a iya amfani da ɓangarorin ilimi da kiwon lafiya wajen cimma buƙatu masu muhimmanci ga rayukan al’umma.

Osinbajo ya kuma ce akwai buƙatar a samu jagoranci mai tsari game da kowane mataki za a ɗauka, ya na mai bada misali da rashin samuwar sa da aka yi a zanga-zangar da ta gabata a Nijeriya.

A madadin a taiƙatu a iya zanga-zanga, ya ce ya kamata a samu wasu hanyoyi a siyaysance da za su taimaka wajen cimma nasarar kawo gyara a ƙasar.

Ya yi kira da a sabonta tsarin ilimi a Nijeriya ta yadda za a fifita haɗin-gwiwa da nazari mai zurfi sama da gasa don samar da ci-gaba acikin al’umma da haɗin-kai mai amfani.