Zargin ƙulla maguɗin zaɓe: Atiku ya fayyace komai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga wani faifan murya da aka yi masa na zargin cewa yana shirin yin maguɗi a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023, a zaɓen shugaban ƙasa.

An zargi abokin takarar Atiku kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, tare da shugaban jam’iyyar PDP na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa (PDPPCC), da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal.

Da yake mayar da martani, kakakin jam’iyyar PDP, Phrank Shuaibu, a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce aikin jam’iyyun adawa ne.

Sanarwar ta ce, “mun yi gargaɗi a makon da ya gabata cewa yayin da zaɓe ke gabatowa, za a samu ƙaruwar yaɗa farfaganda a shafukan sada zumunta. Yayin da ya rage sa’o’i 24 a kaɗa ƙuri’a, mun shaidi farfagandar ba daga jam’iyyar APC kaɗai ba, har ma da LP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *