Zargin ɓata suna: Yadda ta kaya tsakanin Ahmad Pasali da Kannywood

Daga AISHA ASAS

Bai zama wani sabon abu zargi ko ɓata sunan ’yan masana’antar finafinai ta Kannywood ba, amma hakan ba yana nufin sabo da zagin ko barin kowa da halinsa ba.

A Kannywood, mutane da yawa sun saba yin suka tare da aibata musamman ma jaruman, duk da cewa fa suna nishaɗantar da su a lokuta masu yawa, wanda ke sani tambayar, shin ya suke so su kasance? 

A cikin finafinan da suke yi, suna sha’awar ganin su suna kwaikwayon Turawa da Indiyawa, su yi rawa, su sanya ƙananan kaya, kuma duk hakan bai dame su ba, asali ma idan ba hakan aka yi ba, ba su cika kalla ba, amma suna matuƙar sa wa rayuwarsu ido don gano inda suka kuskure su yi masu wankin babban bargo.

Wani idan ka ji ya na zagin ‘yan fim sai ka rantse shi ɗin ba ya saɓa wa Allah.

Ba wai ina ƙoƙarin kare masana’antar fim ba, ko kare jarumanta ba, ina dai so mu fahimci cewa, sana’a ta fim ba sana’a ba ce da ke yawan tunatar da kai Allah, kamar sana’ar karantarwa a Islamiya da sauransu.

Sana’a ce kamar takwarorinta da ke ɗauke da zugar shaiɗan da kuma kusancinsa a tsakaninsu. Kasancewar a duk inda mace da namiji za su haɗu, na ukun su fa shaiɗan ne.

To a irin wannan, da za ka samu mace ta tsuke tana tiƙar rawa, ka dai san ba tarbiyya take koyarwa ba, kuma bai zama adalci ba ka saka ta a rukunin da ka ke sanya malamai ba.

A naka tunanin idan ta bar wurin ɗaukar fim, za ta sa hijabi har ƙasa, da niƙabi, ta nufi gida, ta kwana sallah da neman yardar Allah? Idan hakan ka ke son ganinta ka fara da tambayar kanka ko haka ka ke yi? Ko haka ƙannenka da matanka ko mijinki yake yi?

Dukkanmu masu saɓo ne, don haka mafifita daga cikinmu su ne masu shagaltuwa da yi wa kansu hisabi kan ababen da suke aikatawa, ba wai hango na wani ba.

Ba mai wuta ko aljanna da zai iya saka wani, sai Allah. Kuma idan muka je lahira ka ga ɗan fim a aljanna ba kada ikon ce masa fito, tunda ba gidanku ba ne. Allah ne Ya san tsakaninSa da bayinSa, idan Ya so Ya yi masu gafara, idan Ya so Ya azabtar da su kan ababen da suke aikatawa na laifi.

Kada in yi nisan kiwo har inkasa dawo wa a darasin namu. Kamar yadda da yawa cikin masu bibiyar kafafen soshiyal midiya suka sani, a yan kwanakin baya, kafar TikTok ta ɗauki ɗimi da wasu kalaman ɓatanci ko in ce ɓata suna da wani jarumin TikTok mai suna  Ahmad Pasali, ya yi zuwa ga masana’antar finafinai ta Kannywood, inda har yake jifan kashin kaji ga wasu daga cikin ‘ya’yan masana’antar, ta hanyar kiran suna da aibata su.

Da wannan ne ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya, wato MOPPAN ta tunzura, har ta kasa haƙura da wannan ɓata suna da ake yi wa jarumanta, ta maka jarumin na TikTok kotu, kan zarginsa da ɓata suna da ƙazafi ga wasu jarumai da ma masana’antar Kannywood bakiɗaya.

Kamar yadda jaridar Mujallar Fim ta rawaito, bayan shigar da ƙara kan ɗan TikTok Ahmed Pasali da ƙungiyar MOPPAN ta yi bisa zargin ƙazafi da ɓata sunan ƴan Kannywood, matashin ya bayyana a gaban kotu a Jos.

Pasali ya musanta zargin, wanda ya sa lauyan shi ya nemi a ba da belinsa.

Alƙali Thomas Nakowa ya bada belin tare da gindaya sharuɗɗan beli, ciki har da ajiyar kuɗi N250,000 da samun wanda zai tsaya masa daga Jos, tare da takardun gidan zama. Amma saboda rashin cika waɗannan sharuɗɗa, an mayar da shi gidan gyaran hali har sai an bi ƙa’idojin.

An ɗage sauraron shari’ar zuwa 5 ga Afrilu. Shugaban MOPPAN na ƙasa, Umaru Maikufi Cashman, ya jaddada cewa, ƙungiyar ba za ta lamunci cin mutuncin ƴan Kannywood ba, kuma za su ɗauki mataki kan duk mai yin hakan.

Saidai a ‘yan baya-bayan nan muka ci karo da faifan bidiyon jarumin yana mai bayar da haƙuri kan abinda ya furta wanda ya bayyana kama sunan da ya yi a matsayin kuskure.

Pasali ya fara da yin sallama ga maniyansa, kafin ya ƙara da cewa, “Kwana biyun nan da suka wuce, na yi wani bidiyo yana ta zagayawa wanda na yi akan ‘yan masana’antar Kannywood, Ina mai ba ku haƙuri, abinda ya shafi Ali Nuhu, Adam A. Zango, Bashir Maishadda, Abba El-Mustapha, Sani Danja, da Malam Aminu Saira, da Nafisa ‘Sai Wata Rana’, wato Nafisa Abdullahi, da Rahma Sadau da Hadiza Gabon. 

Ina mai baku haƙuri, saboda na fito, na ambaci sunayenku, na aibata ku.

Ko a addinin Musulunci babu kyau ka fito ka ambaci sunan mutum ka aibata shi. Don haka ina neman afuwanku, ku yafe min, don in ba ku yafe min ba, Allah zai tsayar da ni ranar ƙiyama. Kuma ina neman rahmar Ubangiji.”

Ahmad Pasali, wanda aka sani da Namadina, ya kuma bayyana cewa, ya nemi gafarar jaruman ne alfarmar wannan wata na Ramadan da muke ciki, inda ya kawo hujjarsa da cewa, “Allah Yana fushi da wanda watan Ramadan ya zo bai nemi gafarar mutane ba,” kafin ya rufe da wata ƙissa ta zamanin Annabi Musa da take nuni da rashin dacewar fallasa mai laifi, kasancewar ba a shiga tsakanin bawa da Ubangijinsa. Sannan ya nuna abinda ya aikata a matsayin kuskure da Annabin Rahma (S.A.W) ya yi hani da aikatawa.